Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ce Gwamnatin Tarayya ta raba kayan tallafin shinkafa ga Jihohi 35 duk ta hannun Gwamnoninsu, amma ban da Jihar Kano.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso, ya zargin cewa gwamnatin tarayyar ta mika kason Kano hannun jiga-jigan jam’iyyar APC.
- Shugaban Zimbabwe: Zimbabwe Da Sin Na Da Matsaya Daya A Gaban Kalubaloli
- Kungiyar Miyatti Allah Ta Haramta Kiwon Dare A Jihar Kwara
A cewarsa hakan ya saba wa dimokuraɗiyya.
”Wannan babban cin fuska ne ga dimokUradiyya da kuma tsarin mulkin kasarmu. Wannan mataki dai nuna bangaranci ne da ya wuce gona da iri,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga shugaba Tinubu ya gagguata dakatar da abin da ya kira karan-tsaye ga tsarin dimokuraɗiyya.
Tsohon dan takarar na NNPP, ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ya ce an aike da daraktocin hukumar DSS har guda uku zuwa Jihar Kano, tare kuma da sauya su cikin mako biyu zuwa uku.
Ya ce lamarin na iya zama barazana ga tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp