A halin yanzu Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ta ba wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a garin Maiduguri ta Jihar Borno gudummawar naira miliyan 200 domin su tayar da komatsansu.
Bayanin haka na kunshen ne a sanarsa da aka raba wa manema labarai rabnar Asabar da ta gabata.
- Babban Taron Samar Da Kayayyaki Na 2024 Ya Sa Kaimi Ga Kulla Ayyukan Hadin Gwiwa 718
- Rodri Ba Zai Sake Buga Kwallo A Wannan Kakar Ba Sakamakon Rauni
Manyan manajojin hukumar su 3 suka jagoranci bayar ga cakin kudin ga gwamana Babagana Zulumm a Maiduguri. Manajojin hada da Ibrahim Umar, Ms Bibian Edet da kuma Olalekan Badmus.
A jawabinsa, Shugaban Hukumar NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana cewa, Hukumar na tare da Jihar Borno a daidai wannan lokacin data fuskanci wannan iftilain in da aka yi asarar dinbin rayuka da dukiya na biliyoyin nairori wanda kuma ya daburta harkokin rayuwar a’lumma da dama.
“A matsayin wani tallafin domin saukaka wa a’lumma halin da suka shiga sakamakon ambaliyar ruwa, Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya tare da shawarar Ministan Tattalin Arzikin Teku Adegboyega Oyetola, muke bayar da gudummawar Naira Miliyan 200 domin tallafi ga a’lumma Jihar Borno da ambaliyar ta shafa,” in ji Dantsoho.
Rahoto ya nuna cewa fiye da mutum 414,000 ambaliyar ta raba da matsugunansu yayin da aka kuma aka tabbatar da mutuwar fiye da murum 30 yayin da Dam din Alau ya barke ya yi ambaliya cikin garin Maiduguri da kewaye.