Ambaliyar ruwa ta raba babbar hanyar Bauchi zuwa Kano, wadda ta ke tsakanin Malamawar-Gangara da Babaldu bayan saukar mamakon ruwan sama.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ambaliyar ta dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan titin, wanda hakan ya tilasta wa masu amfani da hanyar zuwa Kano yin dogon zagaye.
- Tinubu Zai Kai Ziyara Equatorial Guinea Ranar Laraba
- Kwanaki 11 Da Hawa Kujerar Mulki, Mataimakin Shugaban Iran Ya Yi Murabus
Wani mazaunin garin Malamawar-Gangara mai suna Isa Usman, ya shaida wa wakilinmu cewa, dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan titin saboda rashin tsaro.
“Kafin ambaliya ta raba hanyar, hanya ce da ta hada Kano zuwa Bauchi amma yanzu babu ababen hawa da matafiya,” in ji shi.
Kazalika, ambaliyar ruwa ta kuma lalata hanyar Azare-Isawa-Giade da ke karamar hukumar Giade a Jihar Bauchi.
Hanya ce da manoman kananan hukumomin Katagum da Giade ke amfani da ita tsawon shekaru da dama.
Hakan ya haifar da firgici da damuwa ga masu amfani da hanyar don yin harkokinsu na yau da kullum.
Idan dai ba a manta ba ambaliyar ta raba hanyar Kano zuwa Maiduguri da ke yankin Maluri-Gaskuri a karamar hukumar Katagum a jihar.