A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron kasa na Qatar.
Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su kara kokari wajen dakile rikicin, da sake fara tattaunawa maimakon akasin hakan.
Dangane da sanarwar da Isra’ila ta gabatar wa Amurka kafin ta kaddamar da harin ta sama, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin da Isra’ila ta dauka na da alaka da rashin daidaito da wasu kasashen suke nunawa a tsawon lokaci kan batun Gabas ta Tsakiya.
Ya ce ana kira ga wasu manyan kasashen duniya da su ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da tabbatar da adalci, da sauke nauyin dake wuyansu, da hada kai da kasashen duniya wajen taka rawa mai ma’ana ta inganta tsagaita bude wuta da saukaka rikicin yankin. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp