Shugaba Vladimir Putin ya gargadi kasashen Yammacin duniya cewa mambobin kungiyar tsaro ta NATO a Turai suna wasa da wuta ta hanyar bai wa Ukraine shawarar ta yi amfani da makaman kasashen Yamma wajen kai hari a cikin kasarsa, lamarin da ya ce ka iya haifar da rikici a fadin duniya.
Sama da shekaru biyu da barkewar wannan yaki mafi muni a nahiyar ta Turai tun bayan yakin duniya na biyu, Putin ya sha yin gargadi kan yiwuwar kazancewar yakin yayin da kasashen Yammaci ke nazarin yadda za a dakile kutsawar dakarun Rasha cikin Ukraine.
- Sinawa Ba Za Su Manta Da Danyen Laifin NATO Na Kai Wa Yugoslavia Hari Ba
- Mece Ce Mafitar Warware Matsalar Ukraine?
Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya shaida wa jaridar The Economist cewa, ya kamata mambobin kawancen su bar Ukraine ta shiga cikin Kasar Rasha da makaman kasashen Yamma, ra’ayin da wasu mambobin kungiyar NATO ke goyon baya amma ban da Amurka.
Putin ya fada wa manema labarai a Tashkent cewa: “Idan wadannan munanan sakamako suka faru a Turai, ta yaya Amurka za ta kasance, tare da la’akari da daidaiton mu a fagen makamai masu mahimmanci.