Ana samun amfanin gona da dama a Nijeriya wadanda ake shukawa su kuma girma a cikin ‘yan watanni. Kazalika, mun yi muku nazari kan amfanin gona guda takwas da ake girbewa cikin watanni shida ko kasa da haka.
Ga jerin amfanin gonar kamar haka:
Waken Suya: Waken Suya na daya daga cikin amfanin gona masu gina jikin dan Adam, yana kuma dauke da sanadarin ‘protein’. Kamar yadda aka sani, ana dafa Waken Suya sannan ana sarrafa busashensa a yi Madara, Fulawa, Awara da sauran nau’ikan abinci.
Haka nan, ana kuma sarrafa shi zuwa Mai, sannan ana kuma ciyar da dabbobi da da shi. Bayan an shuka Irin sa, ana girbe shi daga wata uku zuwa biyar, amma ya danganta da irin yanayi da kuma nau’in Irin nasa da aka shuka.
Shinkafa: Irin Shinkafa da ake shukawa na kaiwa daga watanni Uku zuwa biyar kafin ta girma. Kazalika, tana da saurin yin girma tana kuma kaiwa tsawon kafa uku bayan kwanaki 120, wanda ya yi daidai da lokacin girbe ta, tana kuma samun karbuwa a kasuwannin Nijeriya yadda ya kamata.
Masara: Masara na daya daga cikin amfanin gona da ake yin amfani da ita a matsayin abinci a Nijeriya, sannan ana kuma gasa ta domin ci tare da sarrafa ta zuwa Gurguru. Har wa yau, ana kuma sarrafa ta zuwa fulawa da sauran makamantansu tare da sarrafa ta zuwa abincin dabbobi.
Akasari kafin a girbe ta, tana kaiwa kwanaki 60 zuwa 100 bayan an shuka ta. Kazalika, cikin sauki ake mallakar gonar da ake shuka Masara a Nijeriya, ana kuma shuka Irinta sannan a sayar da ita ga makwabta.
Dankali: Dankali na dauke da sinadarin ‘calories’ dan kadan, sannan mutane da dama na kasar nan na sarrafa shi a matayin abinci tare da yin amfani da shi. Yana daukar watanni biyu zuwa uku bayan an shuka shi. Bugu da kari, ana iya shuka shi a kowacce irin kasar noma.
Tumatir: Ana matukar amfani da tumatir a Nijeriya, ko danyensa ko kuma busasshe. Yana dauke da sanadarin ‘bitamin C’, yana kuma taimakawa wajen rage kamuwa da cututtuka kamar wadanda ke yi wa zuciya illa, ciwon siga da kuma cutar daji.
Ana son a shuka Irinsa a kasar noma mai kyau tare da yi masa ban ruwa. Bayan an shuka Irin nasa, ana fara girbe shi daga watanni 2 zuwa 3, ya danganta da nau’in Irin da aka yi amfani da shi wajen shukawa.
Kankana: Duk yayin da aka shuka Irin Kankana, cikin dan gajeren lokaci ake girbe ta. A Nijeriya, daga wata 3 ake fara girbe ta, sannan ana iya shuka Irinta a kowanne bangare na fadin wannan kasa. Wakazalika, kankana na dauke da sinadarin ‘bitamin A’ da kuma ‘bitamin C’ mai yawan gaske.
Tattasai: Bayan shuka Irin tattasai, ana girbe shi cikin watanni uku kacal. Kazalika, ana iya cewa kusan kowane gida a fadin Nijeriya na yin amfani da shi. Ana kuma sayar da tattasai a kasuwanni da dama a wannan kasa, sannan wadanda ke yin sana’arsa na matukar samun rufin asiri ko kudaden shiga. Hatta a bayan dakin gidanka, za ka iya shuka Irin Tattasai ya girma ya kuma bayar da abin da ake so.
Kokumba: Kokumba na daya daga cikin sanannin kayan marmari ko lambu, ana kuma yin noman sa a wurare da dama na fadin Nijeriya. Wasu na cin sa tsurarsa, domin alfanun da yake da shi musamman a fannin kiwon lafiya. A duk lokacin da aka shuka Irinsa yana da matukar saurin yin girma, ana kuma girbe shi bayan akalla watanni 3. Sannan yana da saurin tafiya a kasuwa, ma’ana mutane suna son sa kwarai da gaske sakamakon amfaninsa ga lafiyar dan Adam.