Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai yi bayani ne akan amfanin Kabewa a jikin mata:
Kabewa tana da amfani sosai a jikin mace, yana temaka wa mace, tana da tasiri sosai ga mace, yana wanke mara tana wanke mahaifa duk wani datti dake jikin mace koda al’adar ta tana wasa in cuta ne Kabewa da hulba da Habbatussauda yana magani da izinin Allah.
Abubuwan bukata:
Kabewa da madara
Yadda za ku hada:
Idan kuka samo Kabewa sai ku yanka ta ku fere bayanta, sannan kun wanke ta, sai ku zuba ta a tukunya ku sa mata ruwa a dafa ta kamar yadda ake dafa ta miya, idan ta dahu sai ku sauke ta ku kwashe ku zuba a bilanda ku nika ta ta yi laushi sai a zuba madara ta ruwa a sha.
Sannan a hada Kabewa da hulba da Habbatussadat ta tafasa ana sha tana da kyau sosai tana maganin duk wani cutittaka dake jikin mahaifa.
Sannan ki samu kanunfari da minannas da asuwakin mata, ki hada su waje daya ki tafasa su ki rinka sha yana gyara mace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp