Kiwon Salwa na kara zama sananne a yau da kullum, domin kuwa ta na da matukar amfani, sannan kuma fanni ne da za a iya samun karin kudaden shiga a kan lokaci.
Salwa na samar da nama da kuma kwai, musamman ganin cewa, ana yawan bukatar naman da kuma kwanta a kasuwanni.
Babban Amfanin Kiwon Salwa
Ba su da wuyar kiwo, domin yawancinsu kanana ne kuma ba su cika bukatar sai ana ba su kulawa ta musamman ba.
Tana Tafiyar Da Kasuwanci:
Salwa na kara tafiyar da kasuwanci yadda ya kamata, sannan kuma tana samar da kudaden shiga ga wadanda suka rungumi kiwon nata.
A ka’ida, Salwa na kammala girmanta ne daga sati shida, inda kuma ta ke fara yin kwai daga sati shida, sannan za a iya fara sayar da wasu daga cikin kwanta, don samun kudaden shiga.
Kula Da Ita:
Salwa ba ta cika bukatar wata kula wa ba, domin tsintsaye ne yan kanana kuma ba su cika bukatar sararin wajen da za su dinga watayawa ba.
Salwa Ba Ta Cika Bukatar Abinci Mai Yawa Ba:
Ba ta cika yawan bukatar abinci ba, idan aka kwatanta ta da sauran tsintsayen da ake kiwatawa, don kasuwanci ba.
Cututtuka Ba Su Cika Harbin Salwa Ba:
Cututtuka ba su cika harbin Salwa ba, sabanin sauran tsintsayen da ake kiwatawa, don kasuwanci ba, haka nan ba ta cika yawan yin rashin lafiya ba.
Ana Yawan Bukatar Namanta:
Ana yawan bukatar naman Salwa tare da kwanta a kasuwanni, musamman ganin tana dauke da sinadarin ‘fat da protein’. Haka nan, namanta na taimakawa wajen yin maganin cututtuka kamar hawan jini, tarin fuka, ciwon suga da sauran makamantansu.
Ribar Da Ake Samu A Kiwon Salwa:
Akalla ana sayar da kwanta a kan farashi mai yawa, sannan kuma tana saka kwai a kullum, iya girman kwanta iya farashinta.
Matakan Fara Kiwon Salwa Don Kasuwanci:
Kiwon Salwa na da matukar muhimmanci, don kuwa namanta da kwanta; ana matukar bukatarsu, domin idan kana da macen Salwa guda 600, za ka iya samun akalla kwai 11,000 a wata guda kacal.
1- Jari: Ya zama wajibi ka kasance kana da jari kafin ka fara kiwon Salwa, musammna domin ka samu cin nasara a kasuwancinka.
2- Samar Da Wajen Kiwonta: Ya kamata ka samar da wajen da ya dace domin kiwon ta, musamman wajen ya kasance waje ne da suka fi bukata.
3- Tanadar Kayan Kiwo: Ya kamata ka tabbatar da ka mallaki kayan da suka dace na kiwon ta, musamman kayan ba su ruwan sha da kayan zuba musu abinci da kuma idan ta tashi yin kwai.
4- Ciyar Da Ita Abinci: Yana da kyau ka ciyar da ita abinci yadda ya dace, duk da cewa ba su cika damuwa da cin abinci mai yawa ba.
5- Tanadar Mata Da Magunguna: Yana da kyau ka tanadar mata da magungunan da za ka rika ba su yayin da suka harbu da wata cuta.
6- Kasuwancinta: Yana da kyau ka sanar da abokan cinikinka, ka sanar da su cewa kana kiwon Salwar, don su saya, za ka kuma iya kai ta gidajen sayar da abinci ko Otel-otel don sayarwa ko kuma ka kai kasuwa.
Shin Ana Samun Riba A Kiwon Salwa?
Tabbas ana samun riba mai dimbin yawa daga kiwon tsintsun Salwa, amma kafin ka fara kiwon, ana so ka tabbatar da ka yi tsarin kasafin kudaden da za ka kashe, kazalika idan za ka yi wannan kiwo; ba sai ka zuba wani jari mai yawa ba, domin za ka iya farawa da ‘yan kudade kadan.
Tsawon Wane Lokaci Salwa Ke Kaiwa Kafin Ta Girma?
Tana da saurin girma, sannan kuma ta kasance daya daga cikin tsintaye masu saurin girma, daga lokacin da ta fara yin kwanta har zuwa girmanta tana kai wa sati shida, kazalika daga sati tara zuwa sha biyu, za a iya cin namanta.
Sai dai, wasu sun fi fara cin namanta daga wata tara zuwa sha biyu.
Sau Nawa Ya Kamata A Ba Ta Abnici?
A kowace safiya ya kamata a tanadar mata da wadataccen abinci, haka nan ana so a koda-yaushe ta kasanace ana tanadar mata da abinci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp