Manhajar Gmail daya ne daga cikin ’email serbice probider’ da kamfanin Google ke gudanar da shi. Ga mai amfani da wayar Android ‘email’ na kamfanin Google (Gmail) zai fi yi masa amfani fiye da sauran ‘probiders’ irinsu Yahoo, Hotmail, Yanded, outlook da sauransu.
 Da yawan mutane in an ce Google, sukan takaita shi da ‘searching engine’ ma’ana wurin da za ka yi browsing (bincike) na wani abu, in kuma aka ambaci ‘Gmail’, da yawa mukan takaita aikinsa da turawa ko karbar sakon ‘email’ da ajiye lambar waya, amma duk amfaninsa ya wuce nan.
- Rikicin Nijar: Tinubu Ya Aika Janar Abdulsalami, Sultan Na Sokoto Zuwa Yamai
- Yadda Maryam Shetty Ta Kadu Da Labarin Cire Sunanta Daga Jerin Ministocin Tinubu
Google shi ne kamfanin da yafi kowane kamfani karfi a duniyar fasahar sadarwa. Shi ne kamfani da yake gudanar da OS (operating system) na Android tare da shi da sauran wasu kamfanoni. Android shi ne OS da mafi yawancinmu muka fi amfani da shi a wayoyinmu na Samsung, Pidel, Tecno, Infinid, Itel, Diomi, Gionee, Huawei, HTC, Motorola, Oppo, Nokia, Bibo da sauransu.
Idan ka bude ‘Gmail Account’ kai tsaye ka yi rijista ne ‘Google account and serbices’, ma’ana za ka yi amfani da duk wani tsare-tsare da manhajoji 131 da Google ke gudanar da su (about.google/products), wadanda iya mai Google account ne kadai zai iya morarsu kai tsaye dari bisa dari.
Wadannan manhajojin sun hada da Gmail, Playstore, YouTube, Google Dribe, Photos, Blogger, Forms, Alerts, AdSense, Google Chats, Google classroom, Family Link, Find My Debice, Google Groups, Contacts, Message, Google one, Podcast, Hangouts, Scholar, Meet, AdMob, Cloud, Translate… da sauransu. Kuma ana amfani da su wajen tura sakonni, karatu, kasuwanci, debeloping, taruka, adana bayanai, kididdiga da sauransu.
Mallakar ‘Google account’ yana taimaka wa wajen Auto-Fill na Login Credentials (bayanai da za ka shiga domin bude wani shafi, wato (username da password); ma’ana, idan ka yi sabing bayanan shiga wani shafi (kamar Facebook ko Twitter), babu bukatar sai ka yi typing na ‘username da password’, a’a kai tsaye Auto-Fill zai shigar maka da bayanan.
Ba za mu iya bayanin dukkan ‘Manhajoji 131′ ba a yanzu, ba kuma lalle a ce sai ka iya amfani da dukkanin manhajojin ba (ya danganta da wanda kake bukatar amfani da shi), sannan wasun su ba a iya amfani da su a wasu kasashen.
Ga bayanin wasu atakaice:
PLAYSTORE– Rumbu ne mai dauke da manhajojin Android (apk) 2.59 million (Statista, 2022). Mai Google account (Gmail) ne kadai zai iya shiga domin sauke ‘apps’ daga cikin Play store.
GOOGLE CONTACTS – ‘App’ ne da ake iya adana lambobin waya daga 1 zuwa 25,000. Amfani da ‘Google Contact’ na da matukar muhimmanci, saboda ko an sami akasi wayarka ta bata, ko lalace, ko aka sace, da zarar ka sami wata wayar ko a computer za ka iya dawo da duk ‘lambobin wayarka’ da ka adana (sabing) a cikinsa.
BLOGGER– zaka iya kirkirar ‘blog site’ da Blogger, har kana iya wallafa rubutu kyauta. Idan kana samun traffic da yawa, za ka iya ‘rijista’ da ‘AdSense’ ka fara samun kudin da Blogger din, musamman idan kana dora talla/ads (misali, leadership.blogspot.com).
FIND MY DEBICE – manhaja ce da za ta taimaka wajen gano inda wayarka take, idan ka rasa ta, ko ka jefar, ko aka sace.
YOUTUBE – wannan sananne ‘app’ ne na Google da za ka iya bude ‘channel’ da shi ta hanyar amfani da ‘Google Account’. Idan kana samun traffic da yawa, akalla subscribers 1000. kuma aka samu an bude ‘contents’ na ka kamar sau 4000, za ka iya fara samun kudi da YouTube.
GOOGLE PHOTOS – Wannan manhajar tana taimaka wa sosai wajen adana hotunan cikin waya. Idan kana ‘backup’ na hotuna a cikin ‘Photos’ za a iya ‘restoring’ nasu a kowace irin waya ka canza, a kowane lokaci.
GOOGLE DRIBE – wannan manhajar ‘cloud’ ce da ke iya bawa mutum damar ajiye ‘files’ a ciki. Suna bawa kowane user (mutum) ‘storage’ na 15 gigabytes. Za ka iya bude abubuwa da ka adana a cikin Dribe a kowace waya ko computer idan ka yi amfani da ‘Google Account’ (Gmail) naka.
SCHOLAR – Google scholar kamar ‘Google searching engine’ ne. Yana taimaka wa wajen lalubo metadata (ta rubuce-rubuce na ilimi).
Misali, idan ka sami wani rubutu, kuma kana son ba shi ‘reference’ idan ka dauki ‘jumla’ ka dora a scholar zai baka irin wannan jumlar ta bayyana a rubuce-rubuce da suka gabata, cikin littattafai, ko mukala (articles), ko journals, ko mujalla da sauransu.
CHROME REMOTE DESKTOP – manhaja ce da za ta ba ka damar shiga cikin files na computer daga wayarka, ko da ba ka tare da computer din.
GOOGLE ADS – Manhajar AdSense da AdMob na taimaka wa masu amfani a social media yin rijista domin samun kudi ta hanyar dora talla a shafukansu (ads).
MEETS – Kamar zoom yake, ana iya yin meeting online.
Akwai sauran apps na Google da za su taimaka sosai wajen debeloping, kamar optimize, Google Analytics, Google Cloud, Firebase, Flutter, Play Protect, Play Games, Surbey, Web da sauransu.
Akwai apps na Google da za su taimaka wajen editing na hoto, SNAP SEED da PHOTOS. Akwai na duba taswira (map), GOOGLE MAP da GOOGLE EARTH. Akwai manhajar karbar bayanai ta GOOGLE FORMS, akwai manhajar fassara ta TRANSLATE. Akwai manhajoji da yawa na GOOGLE, sai a hankali ko in bukata ta tashi, za mu dauki wasu muna bayaninsu a takaice.
Yawancin wadancan tsare-tsare na Google, iya masu Google account (Gmail) ke iya morarsu sosai. Ana iya amfani da Gmail, kamar sauran ‘probiders’ (Yahoo, Hotmail…) wajen yin rijista ko cike-ciken da ake yi a yanar gizo, kamar bude profile na makaranta ko cike aiki (job application), ko cike tallafi, misalin, surbibal fund da sauran cike-cike. Kar ka yi gangancin ba wa kowa Login details na Gmail naka, domin za a iya shiga (accessing) dukkan wadancan tsare-tsaren da shi.