Yadda Allah (SWT) ya halicci Dan’adam, kashi 60 cikin 100 na jikin namiji ruwa ne zalla, inda mace kuma kashi 55 cikin 100 na jikinta shi ma ruwa ne.
Don haka, wannan yana nuna cewa; fiye da rabin jikin Dan’adam ruwa ne, saboda haka; da zarar an ce babu wannan ruwa a tare da mu, kenan babu rai ko kuma rayuwa kwata-kwata.
- Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani
- ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi
Har ila yau, shan ruwa na da matukar amfani tare da mutane, domin kuwa a kullum ruwa na fita daga jikinmu, musamman idan muka je yin fitsari ko bayan gida ko yin zufa, kai har ma yayin da muke yin numfashi.
Kazalika, ana bukatar da namiji ya sha ruwa akalla kimanin lita 3.7 a kullum, mata kuma su sha lita 2.7 a kowace rana. A nan, ana auna yawan ruwan da mutum yake sha ne, wanda ya hada da shayi ko lemo ko kuma jus da sauran makamantansu.
Idan kuma zallan ruwan mutum zai sha kamar ‘Pure Water’, ana so namiji ya sha kamar leda bakwai da rabi, mace ita kuma ta sha kamar leda biyar da rabi.
Amma a nan, ana magana ne a kan lafiyayyu, wadanda kuma ba su da cikakkiyar lafiya, kamar masu ciwon zuciya ko koda, bai kamata su sha wannan adadi ba.
Har ila yau, rashin yawan shan ruwa yadda ya kamata; zai iya jawo wa mutum illoli daban daban. Na farko, rashin shan ruwa a-kai-a-kai zai iya haddasa wa mutum kamuwa da cutar sanyin fitsari (Urinary track infection).
Na biyu kuma, zai iya haddasa wa mutum cutar tsakuwar koda (Kidney stones), a nan wasu abubuwa ne ke dunkulewa su ki fita, sai su zama kamar dutse, wanda hakan ke sanya wa mutum ya rika yin ciwon ciki mai zafi tare da yin fitsarin jini da sauran makamatantan wasu matsaloli da dama.
Na uku kuma, rashin yawan shan ruwa na iya jawo rashin iya yin bayan gida, wanda hakan kan kawo matsalar basir da sauran makamantansu, sakamakon sakaci da yawan shan ruwa.
Don haka, ya zama wajibi mu kula da shan shan ruwa a-kai-a-kai yadda kuma ya kamata, domin kaucewa haduwa da ire-iren wadannan cututtuka, kamar yadda a koda-yaushe likitoci suke kokarin fadakarwa tare da jan hankalinmu.
Lafiya uwar jiki, babu mai fushi da ke, sannan idan kunne ya ji; Hausawa suka ce, wai gangar jiki ta tsira. Don haka, a daure a kula sosai da shan ruwa, saboda irin matukar amfanin da yake da shi.