Daga ranar 18 zuwa 19 ga wata, an gudanar da kwaryar-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33 a Shenzhen, birnin da ke kudancin kasar Sin, wanda kuma ya jawo hankalin duniya. Fiye da shekaru arba’in da suka wuce, nan karamin kauye ne kawai a bakin tekun kudancin kasar Sin. Amma ga shi a yau, ya zama wurin da ba za a iya kyale shi ba a fadin duniya ta fuskar kirkire-kirkire.
Rukunin birane masu kirkire-kirkire na “Shenzhen–Hong Kong–Guangzhou”, yana kan gaba a jerin irin rukunoni 100 da suka yi fice na duniya da Kungiyar Kula da Hakkin Mallakar Ilmi ta Duniya (WIPO) ta fitar.
Yayin da aka mayar da hankali kan batutuwan kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital da kirkirarriyar basira wato AI a taron na wannan karo, lallai watakila babu wani birni da ya fi Shenzhen dacewa. Halin Shenzhen ya kusan zo daya da manyan fannonin fifiko guda uku da aka kafa a taron na bana, wato bude kofa, kirkire-kirkire da kuma hadin gwiwa. A nan birnin, aka kafa kamfanoni da yawa da suka yi suna a kasuwannin duniya, ciki har da Huawei da Tencent da BYD da DJI da sauransu, wadanda zuwa yanzu har suka zama ginshikin tattalin arzikin dijital da sabbin makamashi da kuma kere-kere na zamani.
Sakamakon yadda birnin ke da cikakken tsarin samar da kayayyaki, da kuma halinsa na rungumar gyare-gyare, birnin ya zamanto filin gwaji ga masana’antu na zamani.
Mun fi iya fahimtar halin birnin bisa alkaluman da aka samar, wadanda suka shaida cewa, a shekarar 2025, jimillar GDP na birnin ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 3.87, kuma yawan mazaunansa ya zarce miliyan 18. A bara kuma, jimillar cinikayyar shige da fice ta birnin ta kai yuan tiriliyan 4.55, wato ke nan ta kasance ta farko a cikin biranen babban yankin kasar Sin cikin shekaru da yawa a jere.
Ban da haka, kasashe da yankuna 180 na duniya sun zuba jari a nan, kuma sama da kamfanoni 340 daga cikin fitattun kamfanoni 500 na duniya suna gudanar da ayyuka a Shenzhen. Har ila yau, Shenzhen ya kuma kasance muhimmiyar cibiyar masana’antu masu fasahohin zamani ta kasar Sin.
A shekarar 2025, kason kudaden jarin da birnin ya zuba ta fuskar nazari da kirkire-kirkire ya kai kashi 6.67%, wanda ya kasance na farko a cikin biranen kasar Sin. Hakika, alkaluman sun nuna yadda birnin Shenzhen ke dukufa a kan bude kofa da kirkire-kirkire da kuma hadin gwiwa.
Daga karamin kauye na da, zuwa birnin da yanzu haka ake kallonsa a matsayin “Silicon Valley” na kasar Sin da birnin gaba, ma iya cewa bunkasuwar Shenzhen abin al’ajabi ne. Birnin ba kawai ya rubuta wani babi mai ban sha’awa a tarihin kasar Sin na yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare ba, ya kuma samar da misali ga yankunan Asiya da tekun Pasifik har ma da kasashe masu tasowa na duniya. Kamar yadda kafar yada labarai ta CNA ta kasar Singapore ta bayyana, Shenzhen, a matsayin misali na yadda kasar Sin ke inganta bude kofarta ga ketare, ya zamanto injin kirkire-kirkire na yankin daga yadda ya kasance yankin da aka fi samun masana’antun kere-kere na gargajiya, kuma yadda aka zabi Shenzhen a matsayin wurin da ke karbar bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC na bana ya nuna niyyar kasar Sin ta inganta bude kofa da hadin gwiwa da kasashen duniya.
Sauyin da ya faru a Shenzhen ya shaida yadda kasar Sin ta bunkasa cikin shekarun baya bayan nan da ma inda kasar za ta dosa. Taron APEC da birnin Shenzhen ya karbi bakuncinsa a wannan karo, zai kuma shaida yadda kasar Sin ta hada kai da bangarori daban daban, a kokarin samar da mafita ta tabbatar da zaman lafiya da hadin gwiwa da ci gaban kowa a wannan zamanin da muke ciki.













