Abokai, “duniya a zanen MINA” na mai da hankali kan taron koli na kasashen nahiyar Amurka a yau.
Kwanan baya, Amurka ta karbi bakuncin shirya taron kasashen nahiyar Amurka, don shigar da wasu kasashen Latin Amurka a cikin kungiyarta.
Amma, gwamnatin Biden ta hana kasashen Cuba da Venezuela da Nicaragua da su shiga taron, ba shakka mataki na babakere da nuna bambanci ne, abin da ya jawo rashin jin dadin sauran kasashen Latin Amurka, don haka sun kin yarda su halarci taron.
Wannan taro dake cike da nuna bambanci da yunkurin cimma burin wasu ‘yan siyasar Amurka ba za su samun nasara ba. (Mai zane: Amina Xu)