Shugabar sabon bankin samar da ci gaba na NDB Dilma Rousseff, ta ce kokarin da kasar Amurka ke yi na warware tarin matsalolinta, da matakan babakere da kudin kasar dala ta haifar ba zai haifar da da mai ido ba. Maimakon hakan, matakin zai kara illata Amurkan ne kawai.
Rousseff, wadda ta bayyana hakan yayin wata zantawa da kafar CMG ta kasar Sin, ta ce matakan kakaba haraji da Amurka ta ayyana a ranar 2 ga watan Afrilun da ya shude, sun sanya kasashe da dama fara jingine dalar Amurka, sai dai kuma Amurka ta karkata ga zargin wasu kasashe da laifin hakan. Ta ce kasuwar hada-hadar kudade ta duniya ta shiga yanayi na tangal-tangal da ba ta ga irinsa ba cikin gomman shekaru, kana darajar dalar Amurka ta fadi, su ma kasuwannin hada-hadar hannayen jari sun gamu da koma-baya, yayin da takardun lamani na baitulmalin Amurka suke fada yanayi na rashin tabbas. Rousseff ta yi imanin cewa, gibin cinikayya da Amurka ke fama da shi a halin yanzu, ba shi da nasaba da batun haraji.
- Dakataccen Gwamnan Ribas Ya Dawo Daga Hutun Makonni Biyu A Kasar Waje
- Bayan Fara Binciken $2.96bn, An Samu N80bn A Asusun Tsohon Daraktan Kamfanin NNPCL
A nasa bangare, tsohon ministan kudin kasar Faransa, yayin gwamnatin Charles de Gaulle mista Valéry Giscard d’Estaing, ya ce dalar Amurka ta samu matukar fifiko kan sauran kudaden musaya, wanda hakan ya sa kasashe da dama mika kudadensu na asusun ajiya ga Amurka, ba tare da la’akari da tsada ko kudin ruwa ba. Ya ce bisa hakan ne Amurka ta samu damar juya kudaden ajiyar ba tare da biyan kudin ruwa na a-zo-a-gani ba. Kuma hakan na nufin Amurka na da ikon kashe kudade ba kaidi, tare da dorawa kanta tarin bashi.
A yanzu kuma, Amurka na son kawar da dimbin gibin kudaden asusunta, ta hanyar amfani da kare-karen haraji. A baya Amurka ta yi kokarin hakan ba tare da cimma nasara ba, kuma a yanzu ma hakan ne zai sake faruwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp