• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Da Birtaniya Da Australiya Sun Ci Gaba Da Shirinsu Kan Jirgin Karkashin Ruwa Mai Amfani Da Makamashin Nukiliya

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

Ranar 13 ga wata, shugabannin kasashen Amurka, Birtaniya da Australiya sun gana tare da sanar da shirinsu na samar wa Australiya jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya.

Sanarwar hadin gwiwar da kasashen 3 suka bayar ta ce, Amurka za ta sayar wa Australiya jiragen karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya samfurin Virginia guda 3 a farkon shekaru 2030, daga baya kuma ta kara sayar mata jirage 2 na daban. Haka kuma kasashen 3 sun shirya nazarin wani sabon nau’in jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, bisa tushen fasahohin Amurka da Birtaniya.

  • Kasar Sin Ta Nuna Adawa Da Yadda Amurka Ta Kara Sanyawa Kamfanonin Sin Takunkumi

A cewar wani jami’in Australiya, za a kammala shirin baki daya a shekarar 2055, wanda za a kashe dalar Amurka biliyan 245 wajen aiwatarwa.

Kwanaki da dama kafin kasashen 3 su sanar da shirinsu, an gudanar da taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta IAEA na watan Maris a birnin Vienna, inda sakamakon kokarin da kasar Sin ta yi, an tattauna tare da nazarin batun hadin gwiwar da ke tsakanin Amurka da Birtaniya da Australiya kan jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, tsakanin mambobin hukumar karo na 7 a jere. Wasu kasashe sun nuna adawa kan hadin gwiwar kasashen 3.

Amma kasashen 3 sun kau da kai daga damuwar kasa da kasa, sun ci gaba da sanar da shirin nasu, a yunkurin daukar matakin kashin kai, a maimakon cimma daidaito tsakanin bangarori daban daban, sun kara fadawa hanya mai hadari wadda kuma ba ta dace ba.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Muddin aka aiwatar da shirinsu a zahiri, to, tabbas za a illata zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asiya da tekun Fasifik, da yi wa tsarin hana yaduwar nukiliya na kasa da kasa barna, da sa kaimi kan yin takarar makamai, matakin da zai haifar da illoli masu dimbin yawa a nan gaba.

Hakika hadin gwiwar da ke tsakanin Amurka, Birtaniya da Australiya kan jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, ba su ukun kadai ta shafa ba, tana da nasaba da muradun dukkan kasashe mambobin IAEA. Don haka, kamata ya yi mambobin IAEA su tattauna su kuma tsai da kuduri tare. Kafin a cimma daidaito kan wannan batu, bai kamata ba kasashen 3 su kaddamar da shirinsu. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Dage Kidayar Jama’a Zuwa Watan Mayun 2023

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Dage Kidayar Jama'a Zuwa Watan Mayun 2023

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.