Kasashen duniya sun dade da fuskantar “juyin juya hali” da ke da hannun kasar Amurka, wadanda aka kaddamar da sunan “‘Yanci” da “Dimokuradiyya” amma domin neman juyin mulkin kasashen, musamman a kasashen Afirka da gabas ta tsakiya da gabashin Turai da tsakiyar Asiya da sauransu, juyin juya hali da aka sawa sunayen “Rose Revolution” “Orange Revolution” “Tulip Revolution” “Jasmine Revolution” da sauransu.
Sai dai a cikin wadannan al’amura, fasahohin sadarwa na taka muhimmiyar rawa. Sanin kowa ne Kasar Amurka ce ke kan gaba a duniya ta fannin fasahohin zamani, musamman ma fasahar yanar gizo da ta yayata zuwa kasashen duniya a shekarun 1980, fasahohin da suka kuma samar mata tallafi wajen kaddamar da irin wannan juyin juya hali a kasashen da ta ga dama.
Cibiyar tunkarar harin kumfuta ta gaggawa ta kasar Sin da kamfanin kula da tsaron yanar gizo na 360 na kasar a kwanan nan sun fitar da wani rahoto bisa binciken da suka gudanar, inda suka tona asirin hukumar leken asiri ta kasar Amurka da aka san ta da sunan CIA, ta fannin yin amfani da fasahohin yanar gizo wajen kaddamar da juyin juya hali a kasashen duniya.
Misali, Amurka ta samarwa masu kin jinin gwamnati a kasashe kamar Tunisia da Masar, wani boyayyen tsarin sadarwa domin tabbatar da matasa ‘yan adawa masu son kawo tsaiko ga gwamnati, sun gujewa bincike da sa ido daga gwamnatocinsu yayin da suke gudanar da wannan aiki.
Ko da gwamnatin kasashen sun katse harkokin sadarwa a yunkurin hana ayyukan ‘yan adawar, hukumar CIA na iya samar da hidimomin sadarwa gare su, ta yadda za su iya ci gaba da ayyukansu. Alkaluman sun shaida cewa, a shekaru sama da goma, CIA ta riga ta kifar ko kuma ta yi yunkurin kifar da wasu halastattun gwamnatoci akalla 50, tare da hura wutar rikici a kasashe da dama.
Lallai, don tayar da tashin hankali a wasu kasashe har ma da hambarar da gwamnatin kasashen, Amurka ta yi ta rura wutar rikici a kasashen, ga shi kuma matakan da suka dauka da ma fasahohin zamani da suka yi amfani da su, gaskiya sun ba mu mamaki da ma damuwa.
Duk da haka, bayan da aka kaddamar da wadannan juyin juya halin, al’ummar kasashen sun tarar da cewa, abin da ya faru ba kamar yadda aka alkawarta musu ba, a maimakon yanayin kasashensu ya kara kyautata ba, kasashen sun tsunduma cikin mawuyacin hali na tashin hankali da tabarbarewar tattalin arziki da kuma wahalar rayuwa. Yanayin da ake ciki yanzu a Libya da Iraki da Ukraine dai duk sun shaida hakan.
Sai dai kamar Amurka ba ta jin kunyar munanan ayyukanta, har ma tana ganin hakan ya zama dole, duba da yadda mai taimakawa tsohon shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro, John R. Bolton ya yi na’am da rawar da Amurka ta taka wajen kaddamar da juyin mulki a wasu kasashe, a yayin da yake zantawa da manema labarai, har ya ce, juyin mulki a wasu kasashe “ya zama dole wajen tabbatar da moriyar kasar Amurka”.
To, kamar yadda Mr.Bolton ya fada, Amurka ba ta damu da yanayin da kasashen za su shiga bayan “juyin juya hali” ba, abin da kawai take tunani shi ne ko wadanda za su hau karagar mulkin kasashen za su yi mata biyayya, kuma hakan na faruwa ne sakamakon yadda kullum Amurka ke mai da moriyarta a gaban kome. Domin cimma moriyarta, Amurka tana daukar iya matakan da ta ga dama wajen tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe, har da hambarar da gwamnatocinsu.
Daidai da yadda Michael Lüders, marubucin kasar Jamus ya fada, kullum Amurka tana cewa tana daga cikin masu halin kirki, wadanda ke rungumar dimokuradiyya da ‘yanci a hakkin dan Adam, “amma a hakika abin ba haka yake ba, kawai suna bin moriyarsu ne.” (Lubabatu Lei)