• English
  • Business News
Wednesday, September 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Mai Matukar Son Amfani Da Karfin Tuwo Ta Zama Sanadin Tashin Hankalin Duniya

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Amurka Mai Matukar Son Amfani Da Karfin Tuwo Ta Zama Sanadin Tashin Hankalin Duniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Abokai, a ran 24 ga watan nan ne kwamitin nazarin halin zaman lafiya na kasa da kasa dake birnin Stockholm na kasar Sweden wato SIPRI a takaice, ya gabatar da alkaluman yawan kudaden da kasashe daban-daban suka kashe wajen ayyukan soja, adadin da ya nuna cewa, a shekarar 2022, yawan kudaden ayyukan soja da Amurka ta kashe ya kai dala biliyan 877, wanda ya kai kashi 39% bisa na dukkan kudaden da kasashen duniya suka kashe a fannin, hakan ya sa Amurka ta ci gaba da kasancewa a matsayin farko a duniya a wannan fanni.

Wanzar da zaman lafiya da hadin kai, da samun bunkasuwa tare, matsaya ce ta bai daya da kasashen duniya suka cimma, to amma shin mene ne ya sa Amurka ke kashe kudade masu dimbin yawa haka a zamanin da ake rungumar zaman lafiya?
Bisa kididdigar da aka yi, Afghanstan, da Iraqi, da Libya, da Sham, da dai sauran kasashe sun nutse cikin yake-yake, saboda hujjar yaki da ta’addanci da Amurka ta yi amfani da ita a kasashen tun bayan shekarar 2001.

  • An Rufe Zama Karo Na Hudu Na Taron MDD Game Da Bayanai Na Data

Ban da wannan kuma, Amurka ta rura wuta ga wasu kasashe da su hambarar da gwamnatocinsu, abin da ya jefa yankuna da dama cikin tashe-tashen hankula, baya ga kuma yadda take ta karawa rikicin Rasha da Ukraine gishiri. Bisa kididdigar da SIPRI ya yi, yawan tallafin kudaden soja da Amurka ta baiwa Ukraine a shekarar 2022 ya kai dala biliyan 19.9, adadin ya kai matsayin koli da wata kasa ta baiwa wata kasa ta daban a fannin aikin soja cikin shekara daya tun bayan yakin cacar baka.

Abubuwan da suka faru sun shaida cewa, yawan kudaden ayyukan soja masu dimbin yawa da Amurka ta kashe bai kawo wa duniya zaman lafiya ba, wanda ‘yan siyasar kasar suka ikirarin tabbatarwa. A maimakon hakan, wadannan ‘yan siyasa sun haifar da tashe-tashen hankula a duniya.

Idan gwamnatin Amurka ta kashe irin wadannan kudade masu yawa wajen kyautata zaman rayuwar jama’arta a cikin gida, ba shakka al’ummar kasar za su kara jin dadin zaman rayuwarsu. (Mai zane da sharhi: MINA)

Labarai Masu Nasaba

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ter Stegen Ya Kafa Sabon Tarihi A Barcelona

Next Post

Zargin Sin Da Hannu A Ta’addanci A Nijeriya: Tuggu, Makirci Ne Da Kisisinar Turawan Yamma

Related

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

10 hours ago
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
Daga Birnin Sin

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

11 hours ago
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

12 hours ago
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari
Daga Birnin Sin

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

13 hours ago
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
Daga Birnin Sin

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

14 hours ago
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Daga Birnin Sin

Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

16 hours ago
Next Post
Zargin Sin Da Hannu A Ta’addanci A Nijeriya: Tuggu, Makirci Ne Da Kisisinar Turawan Yamma

Zargin Sin Da Hannu A Ta’addanci A Nijeriya: Tuggu, Makirci Ne Da Kisisinar Turawan Yamma

LABARAI MASU NASABA

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

September 17, 2025
Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

September 17, 2025
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

September 17, 2025
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

September 16, 2025
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

September 16, 2025
Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

September 16, 2025
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

September 16, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

September 16, 2025
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

September 16, 2025
Sojoji

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

September 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.