Abokai, kwanan baya, wasu takardun sirri da ake zargin daga hukumar tsaro ta Pentagon ta gwamnatin Amurka ne, sun bulla a shafukan sada zumunta, lamarin da ya sake jefa Amurka cikin abin kunyar leken asiri a duniya. Wadannan takardun sun nuna cewa, Amurka tana yiwa babban sakataren MDD da ma kasashe kawayenta leken asiri.
Duk da aukuwar irin wannan lamari a lokutan baya da dama,amma Amurka ba ta taba daina aikata wannan laifi ba, wannan ya sanya ta zama kasar dake kan gaba wajen leken asiri a duniya, inda take amfani da dabaru uku:
musanta abin da ya faru, da yada labaran karya don kawar da hankalin jama’a tare da boye laifinta, da kuma yin amfani da babakere ko samarwa wasu kasashe moriya don kwantar da hankalinsu.
Duk da yadda aka nuna fushi da rashin jin dadi, Amurka ta yi kunnen uwar shegu da lamarin, bayan da kura ta lafa, sai ta ci gaba da aikata laifinta kamar yadda ta saba.
Sabo da a cikin zuciyar wasu ‘yan siyasar Amurka,batun hakkin Bil Adama da ra’ayin jama’a ba su da wani muhimmanci a wajensu, illa moriyarsu ko ta Amurka kawai, wadannan laifukan da suka bullo, abin kunya ne kawai a gare su. (Mai zane da sharhi: MINA )