Kasar Amurka, ta gargadi ‘yan kasarta da ke zaune a Nijeriya, musamman a Abuja, babban birnin kasar game da fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci, ta kuma bukaci su yi taka tsantsan.
Ofishin jakadancin Amurka, wanda ya fitar da sanarwar ta’addancin, ya wallafa a shafinsa na yanar gizo a ranar Lahadi, ya ce ‘yan ta’addar za su iya kai hari kan gine-ginen gwamnati da wuraren ibada da makarantu da kasuwanni da manyan kantuna da otal-otal da mashaya da gidajen cin abinci da wuraren wasannin motsa jiki da tashoshin sufuri da wuraren ofisoshin Jami’an tsaro da kuma kungiyoyin kasa da kasa.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Wani Mutum Lokacin Da Suka Kai Hari Yankin Maitama Da Ke Abuja
- Da Dumi-Dumi: ISWAP Ta Kashe Mutum 6, Ta Kwace Makamai A Yankin ‘Yan Boko Haram
A cewar sanarwar, “Ofishin Jakadancin Amurka zai ba da rage ayyukansa har sai an samu sabuwar sanarwa.”
Don haka Ofishin Jakadancin ya shawarci ‘yan kasar da su guji duk wani tafiye-tafiye da ba su da mahimmanci. Har ila yau, ta gargade su da su kasance a faɗake, su guje wa cunkoson jama’a, duk da cewa an tuhume su da su ɗauki tsaron lafiyarsu da muhimmanci tare da cajin wayar salularsu idan wani lamari ya faru, gami da ɗaukar shaidar da ta dace.
Amurka dai na ci gaba da bayar da sanarwar tsaro sakamakon yawaitar hare-haren satar mutane da fashi da makami da kuma hare-haren ta’addanci da suka ta’azzara a Nijeriya a ‘yan kwanakin nan.