• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manoma Sun Caccaki Tinubu Kan Ƙarfafa Shigo Da Shinkafa Da Masara Daga Ƙasashen Waje

by Abubakar Abba
3 months ago
Manoma

Manoma a Nijeriya sun nuna matuƙar damuwarsu kan yadda shinkafa da masarar da ake shigowa da su daga ƙasashen waje suka mamaye kasuwannin ƙasar nan, wanda kuma ake sayar da su kusan a farashi guda da kayan abincin da ake noma a cikin gida. 

Manoman wadanda suka nuna takaicinsu a shafin Tiwita, sun ce tsare-tsaren Shugaban ƙasa Bola Tinubu na kashe darajar noman shinkafa da masara a cikin gida. 

Wannan koken nasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da farashin kayayyakin abinci ke ci gaba da sauƙa a sassa daban-daban na ƙasar nan. 

  • Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya — Jega
  • Gwamnati Za Ta Kafa Cibiyoyin Kiwo a Yankuna Shida — Ƙaramin Ministan Noma

Duk da yake jama’a suna nuna jin daɗinsu kan yadda farashin kayan masarufi ke sauƙa, su kuma manoma na nuna hakan a matsayin abun damuwa. Sun ce, kayan abincin na sauƙa ne sakamakon shigo da su da ake yi daga ƙasashen waje. 

Idan za a tuna dai a watan Yuli na shekarar da ta gabata gwamantin tarayya ta sanar da janye takunkumi na tsawon kwanaki 150 ga shigo da shinkafa da masara da sauran kayan abinci da nufin kawo sauƙi wa al’ummar ƙasar nan. 

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

A zagayen duba farashin kayayyakin da aka gudanar a kasuwannin ƙasar nan, ya nuna cewa, farashin 50-kilogramme na buhun shinkafa ƴar gida ana sayar da shi ne a kan naira dubu 65,000 zuwa naira 68,000, inda kuma ake sayar da masara kan naira dubu 35,000 zuwa 37,000 a kan kowani buhu, yayin da na ƙasashen waje ke kaiwa naira 83,000 kan buhu guda. 

Wannan gagarumin ragin da aka samu ya sanya manoman cikin gida na nuna hakan a matsayin ƙalubale ga ci gaba da noman a Nijeriya.

Sai dai kuma babban matsalar da ake fuskanta a harkar noma a Nijeriya shi ne tsadar takin zamani da sauran kayan aikin gona a Nijeriya, lamarin da ke sanya abun da manoman cikin gida ke fitarwa na tsada, amma kuma in sun kai kasuwa farashin nasu sai ya yi gogayya da na ƙasashen waje lamarin da ke sanya jama’a zaɓar na ƙasashen waje musamman saboda rashin gyara yayin dafawa. 

da yake magana kan wannan lamarin, Farfesa Godwin Oyedokun na jam’iyar Lead City da ke Ibadan, ya ce rubibin sayen shinkafa da masarar ƙasashen waje fiye da na cikin gida a kasuwanni na matuƙar shafan manoman cikin gida kuma hakan na sanyaya gwiwar ƙoƙarinsu na gogayyar wadata ƙasa da abinci. 

Ya ce a maimakon a bar manoma su ci gaba da kokawa wanda hakan ba ci gaba ne ga ƙasar nan, akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta nemi manoman su zauna tare da jin damuwowinsu gami da daukan matakan shawo musu kansu domin amfanun kowa a ƙasar nan. 

“Ina bai wa gwamnati shawara ta samar da tsare-tsaren da za su taimaki amfanin gonan cikin gida da ake samarwa, kamar samar da tallafi, samar rance, zuba hannun jari a ɓangaren noma da fasahohin zamanin da za su taimaka wa manoma, hakan zai sanya suke fitar da amfani gona cikin sauƙi.”

Babban shehin malamin bokon ya kuma ce bai wa manoma damarmakin shiga kasuwannin yadda ya kamata zai taimaka musu wajen samun farashi na adalci, ya kuma nemi a horas da manoma kan dabarun noma na zamani da amfani da fasahohi domin ƙara sauƙaƙa harkokin noma a ƙasar nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
Shugabar Tanzania Ta Kaddamar Da Cibiyar Cinikayya Da Jigila Da Sin Ta Gina A Kasar

Shugabar Tanzania Ta Kaddamar Da Cibiyar Cinikayya Da Jigila Da Sin Ta Gina A Kasar

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025
Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.