Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a yau Asabar cewa, furucin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi game da manufar kasarsa kan Sin, ya nuna cewa Amurka ta sauka daga kan turba game da yadda take kallon duniya da kasar Sin, dama yadda take kallon dangantakar dake tsakaninsu.
Ya ce abun da suke son fadawa Amurka shi ne, duniya ba kamar yadda take fasaltawa ba ne, kuma kasar Sin ba kamar yadda take tunani ba ne. Haka kuma, dangantakar kasashen biyu ba na samun nasara daga faduwar dayan ba ne, kamar yadda ita Amurkar ta tsara. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)