Hukumar tsaro ta FBI ta ce tana amfani da fasahar Israila wajen ganin ta yi kutsa cikin wayar maharin tsohon shugaban kasar Amurka, Donal Trump da mutumin ya yi yunkurin halakawa a wani mataki na farko-farko don binciken yadda aka yi yunkurin kashe shi a makon jiya, kamar yadda Washington Post ta rawaito.
Masu binciken sun shiga amfani da ‘Cellebrite’ wajen kutsawa cikin wayar Thomas Matthew Crooks, 20, Bethel, Pennsybania, wanda ya bude wuta ga Trump a wajen gangani a kusa da Butler a ranar Asabar.
- Masu Zanga-zanga Sun Fito Duk Da Dokar Hana Fita A Jigawa
- Yadda Allah Yake Nuna Tausayi Da Girmama Manzon Allah S.A.W (1)
Crooks wanda ya yi amfani da bindigar da mahaifinsa ya saya ba bisa ka’ida ba a shekaru 11 da suka gabata, ya kashe mutum guda da jikkata wasu biyu, kuma daga cikin harsasan nasa har sun shafi kunnen dan takarar shugaban Amurka a kunnensa na dama. Sai dai, nan take wani kwararren maharbin nesa na Amurka ya harbe Crooks nan take.
An samu wayar maharbin a jikinsa kuma an yi kutse cikinta domin taimaka wa masu bincike gano dalilan da suke cikin ransa da kuma manufarsa na neman kashe Trump. Zai iya daukan masu bincike makonni ko ma watanni kafin su iya samun damar kutsawa cikin wayar maharbin, amma ta hanyar amfani da fasahar Israila za su iya samun nasarar gudanar da aikinsu cikin mintuna 40 kacal a cewar rahoton.
Cellebrite, wanda aka jero cikin NASDAK, na fuskantar nazarta daga kungiyoyin kare hakkin Bil-adama tsawon shekaru kan sayar da shi da kuma ayyukansa ga gwamnatocin duniya ciki har da Pakistan da kuma Belarus.
Masu binciken na tunanin cewa maharin wato Crooks ya yi amfani da wayoyi guda biyu, bayan da aka gano wata wayar da baturinta ya mutu a gidansa da ke Bethel Park, inda ke zaure shi da iayyensa.
Makwabta da abokan karatun Crooks sun tabbatar da cewa, Crooks da iyayensa lafiyarsu kalau, wanda wani daga cikin makwabtan nasa ya misalta maharin da cewa, “yana yawan zama shiru”. Sai dai wani da ke kula da shi a makaranta wanda ke aiki da yayar maharin, ya karyata rahoton cewa Crooks zai iya bude wuta a lokacin da yake makaranta. Ya misalta shi a matsayin mutum mai shiru-shiru kuma mai hazaka da bayar da hadin kai, sannan ya iya magana sosai cikin hikima.
Wasu mutum biyu ma sun tabbatar da cewa iyayen Crooks masu son zaman lafiya ne kuma suna da lasisi na aiki wadanda suke zaune da juna lafiya.