Masu karatu assalamu alaikum. Kafin mu shiga darasinmu nay au, za mu karasa na makon jiya da muke yi mai taken ‘Girman Darajar Manzon Allah (SAW): Darasi Daga “Nuun”.
Bayan Allah ya yabi Manzon Allah (SAW) kamar yadda muka kawo a makon jiya, sai kuma ya sake zargin makiyin Annabin (Walidu bin Mugira) da fadar mummunan halin makiyin. Allah ya dinga kirga aibobinsa. Ya aibaci Manzon Allah ne da Kalmar “mahaukaci”, a’uzu billahi. Sai Allah Ta’ala ya dinga yi ma sa tonon silili yana fadar aibobinsa a jere; daya-bayan-daya yana kare wa Manzon Allah. Allah ya lissafa abubuwan zargi ga kafiran sama da goma. Allah ya ce wannan da ya fada maka cewa kai mahaukaci ne, na yi ma rantsuwa kai ba mahaukaci ba ne, to shi bari ka ji irin sa: “Kar ka bi shi; makaryaci ne (Mu’umini zai iya yin wasu abubuwa marasa kyau amma ba zai karya ba. Karya mummunar aba ce). Kullum abin da yake buri shi ne ka sayar da lahirarka a kan duniya (kamar yadda ya sayar da tasa. Wannan shi ne almundahana, wato mutum ya mika lahirarsa saboda duniya). Kar ka bi dukkan mai rantsuwa wulakantacce (da ya yi magana kadan sai ya dinga rantse-rantse, ya ce ya rantse da Lata, ya rantse da Uzza. ‘Yan’uwansa kafirai suna jin haka sai suka ce wannan da Walidu ake yi. Da suka zo suka fada ma sa sai ya ce kwarai abin da Muhammadu ya fada gaskiya ne). Mai yawan zunde (yi da wani, mutum ya rika fadar laifin wani. A wurin Turawa wannan ba laifi ba ne, duk abin da wani ya yi in dai gaskiya ne a fito fili a fada, amma a Musulunci ba a son yada fasadi) mai annamimanci (yada jita-jita). Mai hana alheri, mai shisshigi, mai sabo. Mai kakkausan hali, bayan haka dan zina ne.”
Da ayar cewa dan zina ne ta sauka, Walidu ya ce duk abin da aka fada a kansa (a ayoyin baya) gaskiya ne, amma abin da aka fada na cewa shi dan zina ne bai san maganar ba. Mugira shi ne babansa; amma kuma Kur’anin Muhmmadu ba ya karya da aka ce ma sa shi dan zina ne. Sai ya zare takobinsa ya nufi wurin uwarsa ya ce ma ta ga abin da Kur’anin Muhammadu ya fada (cewa shi dan zina ne) kuma Kur’anin ba ya karya, ya abin yake ne? Sai uwar ta ce “i, babanka mai kudi ne na tashin hankali a Makkah amma kuma ba ya iya saduwa da mace. Ni kuma na ji tsoron kar kudin ubanku ya tafi sai na tafi wurin mai kiwon dabbobi na gidanku shi ne aka haife ka”. Daga nan ya ce “haba wannan kuwa, don na san Kur’anin Muhammadu ba ya karya”. Amma kuma kamar yadda Allah yake fitar da haske daga duhu, Walidu yana da da babba a Musulunci, Khalid bin Walid. Dama lamarin iyaye bai shafar ‘ya’ya. Idan kafiri ya musulunta, musulunci ya zama ubansa. Idan shege wanda ba shi da uba yana kafirci ya musulunta, yanzu musulunci shi ne ubansa.
Allah Ta’ala ya zargi makiyin Annabi (SAW) da wadannan abubuwa na banza da yawa har zuwa ayar da Allah ya ce “idan an karanta ma sa ayoyinmu sai ya ce tatsuniyoyin farko ne”. Sannan Allah ya cika wannan magana da narko na gaskiya da cikar tsiyar wannan mutumin, da cikar halakarsa a wurin da Allah ya ce “za mu yi ma sa alama a kan karan hancinsa”. Kila an ce a ranar Yakin Badar an yanke hancinsa, kila kuma aka ce ya rasu kafin ranar yakin amma Allah ya kawo bala’in da ya yanke hancinsa.
Idan aka yi la’akari da duk wadannan, Allah ne da kansa (SWT) ya taimaki Manzon Allah a kan kafiran, ya rika kare ma sa kuma hakan sai ya fi cika da kai matuka bisa ga a ce Manzon Allah ne yake kare wa kansa. Sauran Annabawa da kansu suke kare wa kansu, amma Manzon Allah (SAW) Allah ne ya yi ma sa. Kuma wannan shi ya fi tabbata a cikin janibin girman Manzon Allah.
Ya ‘yan’uwa Musulmi mu yi hankali da taka-tsan-tsan a kan furta kalamai na rashin girma ga Manzon Allah (SAW). Domin tun daga ranar da Allah ya fadi wadancan maganganu a kan Walidu bin Mugira, duk idan ka ga makiyin Annabi (SAW) sai ka same shi da wadannan munanan dabi’un. Don haka kowa ya yi hankali, duk wanda ya fada wa Manzon Allah irin miyagun kalaman da makiya suka gaya ma sa, za ka gan shi da wadannan miyagun dabi’un. Allah ya kiyaye mu da aikata hakan.
Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.
Yadda Allah Yake Nuna Tausayi Da Girmama Manzon Allah S.A.W
Allah ya yi rantsuwa da haruffan da suka zo a farkon Suratu ‘Daa-hee’ (za mu zo wurin da za mu yi karin bayani a kai), daga nan sai Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) “ban saukar da Alkur’ani gare ka ba don ka wahala”. Saboda Manzon Allah (SAW) kwana yake yi yana karatun Alkur’ani. Akwai Sahabin Annabi (SAW) Abdullahi bin Mas’udin (RA), ya ce yana kwadayin wata rana ya ga Annabi yana tsayuwar dare ya bishi, rannan kuwa sai Manzon Allah (SAW) ya fito Masallaci don ya yi nafilfilinsa, ya saba yi a daki amma rannan sai ya fito Masallaci. Abdullahi bin Mas’udin ya ce na je na yo alwala na kabbara na bi shi, na ji ya fara karanta Suratul Bakara, sai na riya a raina cewa kila zai karanta aya dari ya yi ruku’u, sai ya karanta Bakara gaba daya ya shiga Ali Imran, na ce kila a ciki zai yi aya dari, ya gama surar baki daya ya shiga Nisa’i, na ce kila a nan zai yi aya dari ya yi ruku’u, nan ma ya gama ta ya kama Ma’ida. Sahabin ya ce sai da na so in yanke sallar in tafi. Kuma Manzon Allah bai tarar da wata aya ta gafara ba face sai ya tsaya ya nemi gafara, bai tarar da wata aya ta neman sauki ba sai ya tsaya ya nemi sauki, bai tarar da wata aya ta neman tsari ba sai ya tsaya ya nemi tsari (SAW).Da yawa wadanda suka ruwaito tsayuwar daren Manzon Allah (SAW) za ka ji sun ce da ya bude sallar sai ya fara da Bakara, kamar kullum sauka yake yi.
Manzon Allah (SAW) yana yin haka har sai da kafafuwansa suka kumbura, kila Abdullahi bin Mas’udin, kila Abdullahi bin Abbas, kila kuma matarsa Sayyida Aisha (RA) wata rana ta ce masa, wannan kumburin kafar fa ya Rasulallah? Kai da Allah ya ce in da kana da zunubi ma an gafarta maka daga wanda ya wuce har zuwa wanda ma ba a kai ga aikatawa ba. Sai Manzon Allah (SAW) ya ba da amsa da cewar “to ba zan zama Bawa mai godiya ba?”. Ke nan duk wannan abu da Manzon Allah (SAW) yake yi godiya ne. To har dai Allah ya tsara masa daren, ya ce “ka yi tsayuwar daren dan kadan,” ga yadda za ka yi, “raba daren biyu (ko ka yi barci a rabi na farko, daga bayan Isha’i zuwa rabin dare, sannan ka tashi ka yi sallah har asubah, ko kuma ka yi sallar daga bayan Isha’i zuwa rabin dare sai ka yi barci), za ka iya rage wani abu daga cikin rabin da za ka yi barci ka kara wa dayan (na sallah), ko ka rage wani abu daga na sallah ka kara wa na barci (duk Allah ya ce ya yarda). Sannan ka karanta Alkur’ani karantawa.”
To ka ga, saboda tausayin Allah ga Manzon Allah (SAW) sai ya raba masa daren ma. To kuma wani lokaci barcin ma sai ya kwashe shi (SAW). Wani Sahabi ya ba da kissar cewa wata rana muna tafiya da Annabi (SAW) rakumina yana kusa da rakuminsa, sai na ga yana gocewa a hankula kamar zai fado, sai na dan daki rakumina kadan na tokare shi kar ya fadi har ya zauna dai-dai a saman rakuminsa, sai na dawo da baya, ana cikin tafiya sai na kuma ganin ya goce, sai na daki rakumina na zo kusa na kuma tokararsa kadan har ya zauna dai-dai, na sake komawa baya (sai ya ce to na uku fa) sai ya goto kamar zai fadi, sai na daki rakumina da gudu na je na tokare shi, sai (Manzon Allah SAW) ya ce “waye wannan?” Sahabin ya amsa ya ce wane ni ne ya Rasulallah. Manzon Allah (SAW) ya ce masa “lafiya?”, sai Sahabin ya ce ya Rasulallahi gani na yi gyangyadi ya kwashe ka kamar za ka fado shi ya sa na zo na tokare ka. Manzon Allah (SAW) ya ce masa “Allah ya kiyaye ka kamar yadda ka kiyaye Annabinsa.”
Shi Manzon Allah (SAW) sallar dare dole ce a kansa amma sauran al’ummarsa ba dole ba ce. Idan mutum ya so bayan ya yi shafa’i da wuturi sai ya kama barcinsa. Amma kuma ga masu lura, ai kai ba sai an ce maka ka yi ba, domin Manzon Allah (SAW) wanda komai da komai ya samu amma ga shi nan yana yi, ai ya ishe ka ishara. Illa dai kawai kowa ya yi iya karfinsa, kar mutum ya debi mai yawa ya zo ya kasa yi.
To, Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) ba mu saukar maka da wannan Alkur’ani don ka sha wahala ba. Kila an ce ma’anar wadancan haruffan na ‘Daa-hee’ da Allah ya fara rantsewa da su a farkon surar, suna ne daga cikin sunayen Manzon Allah. Kila kuma aka ce ‘Daa-hee’ sunan Allah ne. Kila kuma ma’anar ita ce ya kai cikakken mutum. Kila kuma tana nufin ya kai cikakken Dan Adam, (saboda wasu abubuwan na Alkur’ani Siriniyananci ne irin su ‘zanjabila’). Kila kuma yana daga cikin kuramen baki ne. Idan an tafi a kan Siriniyananci ne aka fassara shi da Larabci, wannan ya sa aka samu fassarar da yawa. Amma kyakkyawar fassarar ‘Daa-hee’ ita ce ‘Allahu A’alamu muraadihi bi zaalik’. Sai dai kuma mun karanto wani Hadisi da Manzon Allah (SAW) ya ce “ina da sunaye guda goma a wurin Ubangijina,” a ciki ya fadi da ‘Yaasiyn’ da ‘Daa-ha’. Wasu Malamai kuma sun ce ma’anar ‘Daa-hee’ haruffa ne yankakku da suka kasance wani sirri a tsakanin Allah Tabaraka wa Ta’ala da Manzon Allah (SAW). A lokacin da Mala’ika Jibrilu (AS) ya saukar da ‘Kaaf-hee-aiyn-saad’, Manzon Allah (SAW) ya ce “na sani (ma’anarsa) – mu cigaba,” ta nan Jibrilu ya san akwai wani sirri a tsakanin Allah da Manzon Allah da bai sani ba.
Kila kuma wani mutum ya tambayi Abdullahi bin Abbas (RA) kan ma’anar ‘Hee-miym-aiynun-siyn-kaaf’ sai ya ce ‘Allahu A’alamu muraadihi bi zaalik’, to akwai Jabir bin Abdullahi a kusa da shi, sai ya kamo wannan mutumin ya ce masa (Abdullahi) ba ya so ya fassara ma ne. Ai ma’anarsa ita ce shi (Abdullahi bin Abbas) da ka tambaya wai Allah zai bashi zurriyya za su zama sarakuna su gina wani gari a tsakanin koramai guda biyu, sunan garin Bagadada, za su yi zalunci dare daya Allah zai halaka su, ita ce ma’anar. Dubi wani sirri na Allah kuma!
Malam Wasidi kuma ya ce abin da Allah yake nufi da ‘Daahee’ shi ne ya tsarkakakke. Harafin farko ‘Damisa-hannu’ farkon sunan Allah ne na ‘Dahiru’ kuma ya ba Manzon Allah shi, sai ‘Hakurin’ kuma farkon sunan Allah ne na ‘Hadi’da shi ma ya ba Manzon Allah (wa innaka la tahdiy ila siradil mustakim, ma’ana wallahi ya Rasulallah kai ma kana shiryarwa izuwa tafarki madaidaici).
Wasu malamai kuma suka ce ma’anar ‘Daa-hee’, harafin farko yana nufin ‘taka’, na biyu yana nufin ‘kasa’, don haka ma’anar ana nufin ya Rasulallah taka wannan kasar, taka kafarka. Saboda Manzon Allah (SAW) idan yana karatu a sallah kafarsa ta gaji sai ya daga daya ta huta, sannan ita ma dayar a daga ta idan ya mayar da waccan har kafafuwansa suka fara tsagewa, shi ne Allah ya ce masa bai saukar da wannan Kur’ani don ya sha wahala ba. Wannan tausayi ne na Allah ga Manzon Allah (SAW).