Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake ɗage shari’ar da ake yi ta shugabannin ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru, Mahmud Usman da Abubakar Abba, zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba.
An shirya fara shari’ar ne a ranar 21 ga watan Oktoba, amma aka ɗage saboda lauyan DSS, Mohammed Abubakar, bai samu damar halarta ba.
- Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
- ’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu
Ya rubuta wa kotu takarda inda ya nemi a ɗage shari’ar, kuma alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya amince.
A baya, kotun ta yanke wa Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari saboda hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Usman ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Okene ne a Jihar Kogi, yayin da Abubakar Abba, wanda ake kira Isah Adam ko Mahmud Al-Nigeri, ɗan asalin Daura, daga Jihar Katsina ne.
DSS ta gurfanar da su bisa tuhumar laifuka 32 da suka shafi ta’addanci.
Usman ya amsa laifi ɗaya kacal na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma ya musanta sauran.
Abba kuwa ya ƙi amsa dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su.
An zarge su da kai hari sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja, sace mutane, samar da kuɗin ta’addanci, da kuma samun horo a ƙasar Mali daga wata ƙungiyar ta’addanci ta waje.
Haka kuma DSS ta ce sun sace jami’in Kwastam da wani jami’in Shige da Fice wanda ya mutu a hannunsu, tare da karɓar kuɗin fansa na miliyoyin Naira daga iyalan waɗanda suka sace kafin a kama su.