Wakilan kasashen Afirka da suka halarci taron karawa juna sani na yankin Afirka, kan amfani da fasahar Juncao a Kigali, babban birnin kasar Rwanda sun ba da shawarar yin amfani da fasahar don bunkasa noma mai dorewa a nahiyar Afirka.
Shugaban reshen tsare-tsare na kasa da samar da kwarewa, sashen SDG, na sashen tattalin arziki da zamantakewa na MDD Amso Sibanda, ya bayyana a wajen taron bitar cewa, fasahar Juncao wani irin shiri ne mai fifiko a karkashin asusun samar da zaman lafiya da bunkasuwa na kasar Sin da MDD, a daidai gabar da yake ba da gudummawa ga manufofi masu dorewa na MDD (SDGs), wadanda suka hada da yaki da talauci, da rage yunwa, amfani da makamashi da ake iya sabuntawa, karfafawa mata samun abubuwan dogaro da kai, samar da ayyukan yi, da matakan yaki da sauyin yanayi da ake ci gaba da yi. (Mai fassarawa: Ibrahim)