Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya gabatar da take da kuma tambarin shirin telabijin na musamman na murnar bikin bazara na shekarar 2024 na kasar Sin, a ranar Asabar, gabanin bikin shekarar Dragon da ke tafe a watan Fabrairun 2024.
An yi amfani da harafi na musamman “龘,” wajen zana tambarin wanda ke nufin “tashin dragon”, a matsayin babban alamar gani. Harafin da aka zaba, wani kwatanci ne da ke nuni da yadda al’ummar Sinawa biliyan 1.4 ke samun bunkasuwa, yayin da dragon din ya zama alama ta ruhaniya ga jama’ar kasar Sin cikin dubban shekaru da suka gabata.
Wani tsohon salon rubutun hatimi na kasar Sin ne ya ingiza wannan zane mai karfi, tsayayye kuma a mike, wanda ke nuni da yanayin al’adun Sinawa mai girma da kuzari. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp