Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC), ta buɗe sabbin cibiyoyin gwaji da killace masu fama da cutar sanƙarau a jihohin Jigawa, Yobe, Gombe, Katsina, Kebbi da Sakkwato.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da adadin mutanen da cutar ta kashe ya kai mutum 151, inda sama da ƙananan yara 60 ke cikin waɗanda suka rasa rayukansu.
- Manufar Hade Aikin Raya Larduna Ita Ce Mabudin Kofar Cimma Zamanantarwa Da Samun Wadata
- Saudiyya Ta Ƙaryata Sabuwar Dokar Hana Biza Ga Nijeriya Da Ƙasashe 13
A cewar NCDC, zuwa ranar 23 ga watan Maris, mutane 1,826 ake kyautata zaton suna fama da cutar a jihohi 23.
Cutar ta fi ƙamari a jihohi 10, musamman Kebbi da ke da mutum 881, Katsina 158, Jigawa 147, Sakkwato 303, Yobe 109, Gombe 47, Borno 36, Adamawa 27, Oyo 23 da kuma Bauchi 66.
Hukumar ta ce ƙananan hukumomi 17 ne suka fi fama da yawan masu kamuwa da cutar, inda kowannensu ya samu fiye da mutane 10 da suka kamu da sanƙarau.
NCDC ta buƙaci jama’a su kula da lafiyarsu tare da kai rahoton duk wani mutum da ya nuna alamun cutar domin samun kulawa da wuri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp