A jiya ne aka bude bikin baje kolin fina-finai na kasa da kasa karo na 25 a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda aka tsara ayyuka 53 da za a ba da lambar yabo ta Golden Goblet ta bana.
Kusan fina-finai 450 daga cikin gida da waje ne za a nuna a gidajen sinima 41 a fadin birnin Shanghai a yayin bikin na tsawon kwanaki 9, nuna fina-finai 53 da suka yi fice a duniya, da sassa kasa da kasa guda 41, da na Asiya 80, da 76 daga kasar Sin, a cewar masu shirya gasar.
Bikin (SIFF) wanda aka kafa shi a shekara ta 1993, wata gasa ce ta duniya inda Shanghai ke kokarin zama cibiyar al’adu ta duniya. Lamarin da ya jawo hankalin duniya baki daya, sakamakon bunkasuwar kasuwannin fina-finai na kasar Sin. (Mai fassarawa: Ibrahim)