A yau Asabar ne aka bude bikin nuna fina-finai na kasa da kasa karo na 12 a nan birnin Beijing.
Shen Haixiong, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin fadakar da al’umma na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar wato CMG, kana shugaban kwamitin shirya bikin fina-finai na kasa da kasa karo na 12 na birnin Beijing, ya gabatar da jawabi, tare da sanar da bude bikin.
Taken bikin fina-finan na wannan shekara shi ne “Zuciya daya, aikata na hakika”, wanda kuma ke gayyatar masu aikin shirya fina-finai daga duk duniya da su hada kai, don amfani da sabbin yanayi, da sabbin sha’awa wajen zana wani tsarin ci gaba mai ban mamaki.
A bikin na bana, babban sashin gasar bikin fina-finai na “Tiantan Award” da aka kafa, ya jawo jimillar fina-finai 1,450 a duniya baki daya da aka yi wa rajista, adadin da ya karu da kashi 63% idan aka kwatanta da na bara.
Daga cikin su, akwai fina-finan kasashen waje 1,193 da suka fito daga kasashe da yankuna 88.
A ranar 20 ga watan Agustan nan ne za a rufe bikin nuna fina-finai na kasa da kasa karo na 12 na birnin Beijing, lokacin da za a ba da babbar lambar yabo guda goma ta “Tiantan Award”. (Mai fassara: Bilkisu Xin)