An gudanar da bikin fina-finan kasar Sin a gidan sinima na Westgate dake birnin Harare na kasar Zimbabwe, bikin da ya hallara masu sha’awar fina-finai da sauran masu ruwa da tsaki, wanda kuma ya alamta musayar al’adu tsakanin Sin da Zimbabwe.
An dai bude bikin ne a jiya Talata, inda aka fara da nuna fim din barkwanci mai suna “Panda Plan”, na shahararren tauraron fina-finan nan dan kasar Sin wato Jackie Chan, fim din da ya yi matukar jan hankalin ’yan kallo, da jami’an gwamnati da mashirya fina-finai.
- Za A Watsa Shirin Talabijin Don Bayyana Tunanin Al’adu Na Xi Jinping
- Sin Ya Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Aiwatar Da Mataki Mai Hadari A Zirin Gaza
Gabanin bikin, mataimakiyar ministan wasanni, shakatawa, raya fasahohi da al’adu ta kasar Zimbabwe Emily Jesaya, ta jaddada muhimmancin bikin a fannin karfafa alakar kasashen biyu a harkar fina-finai.
Yayin zantawarta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Jesaya ta ce bikin na wannan karo biki ne na murnar kyakkyawar dangantakar sassan biyu, kana an zabi gudanar da murnar cudanyar kasashen biyu ta hanyar gudanar da bukukuwan fina-finai ne saboda yadda Zimbabwe ke kimanta rawar da fasahohi, da al’adu ke takawa wajen bunkasa dangantaka.
Jami’ar ta kara da cewa, a gabar da ake kara zurfafa alaka tsakanin Sin da Zimbabwe, bikin na wannan karo ya samar da tarin damammaki na hadin gwiwa a fannin shirya fina-finai da musayar al’adu. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp