Cibiyar koyar da harshen Sinanci da kulla hadin gwiwa ta kasar Sin (CLEC) da jami’ar Cape Coast ta kasar Ghana (UCC), sun bude wata cibiyar horar da malaman koyar da Sinanci na yammacin Afrika.
Da yake jawabi yayin bikin bude cibiyar, Hu Zhiping, mataimakin daraktan cibiyar CLEC, ya ce a baya bayan nan, bukatar koyon Sinanci ta karu a nahiyar Afrika, sanadiyyar karuwar dangantakar tattalin arziki da ta siyasa da al’adu, tsakanin Sin da kasashen Afrika.
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji
- An Jinjinawa Kwarewar Sin A Bikin Nune-Nunen Ayyukan Gona Na Cote d’Ivoire
Hu Zhiping, ya bayyana yammacin Afrika a matsayin daya daga cikin yankuna mafiya samun sauyi wanda kuma raya harshen ke da kyakkyawar makoma. Haka kuma, wuri ne da ake samun karin makarantun dake koyar da Sinanci.
A nasa bangare, mataimakin shugaban jami’ar UCC Denis Aheto, ya yaba da bude cibiyar yana mai bayyana ta a matsayin muhimmin matakin inganta ilimi da musayar al’adu da hadin gwiwar kasa da kasa a yankin.
Ya kara da cewa, tasirin kasar Sin a duniya na karuwa, kuma Ghana ta samu karin dalibai da kwararru dake koyon Sinanci saboda karuwar tasirinsa. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp