Dubban jama’a na jira a iyakar Rafah bayan da aka bude kofofin shiga cikin Masar.
Akwai hotuna kai tsaye na dimbin jama’a da ke jira don wucewa ta kan iyakar.
- Manyan Jami’an Najeriya Sun Amince Da Ci Gaban Hadin Kai Karkashin Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
- Dabarun Samun Kudi Ga Matan Aure Ta Hanyar Fasahar Sadarwa – Hajiya Hafsat
Tun da farko, motocin daukar marasa lafiya sun tsallaka daga Masar zuwa yankin Gaza don tattara mutanen da suka jikkata .
Ya zuwa yanzu mutanen da Hamas ta kama ta sake su ne kadai fararen hulan da suka bar Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba – kasancewar duka hanyoyin a rufe.
An sami rahoton cewa Katar ta kulla yarjejeniya don bai wa wasu mutane daman ficewa daga Gaza, tare da hadin gwiwar Amurka.
Falasdinawa 88 da aka yi wa rauni ne za su bar Gaza zuwa Masar
Daruruwan mutane ciki har da iyalai masu yara suna jira a dauke da jakunkuna a wajen tashar iyakar Rafah zaune a kasa yayin da suke sa ran za a bar su su tsallaka zuwa Masar nan ba da jimawa ba.
Babu alamun motocin daukar marasa lafiya ko wadanda suka jikkata sun shiga Masar, kodayake ana iya samun shirye-shirye na musamman ga wadanda ke bukatar magani.
A cewar hukumomin yankin, ana sa ran za a ba da izini ga mutane 88 da suka jikkata zuwa cikin Masar.
An yi imanin cewa Masar na shirin kafa wani asibiti mai nisan kilomita 10 daga kan iyakar. To amma rahotannin da suka bayyana a yau na nuni da cewa, a halin yanzu motocin daukar marasa lafiya na dab da shiga Masar da wadanda suka jikkata daga Fadasdinu.