A ranar 23 ga wata, an bude taron dandalin tattaunawar Afirka ta yamma karo na farko a birnin Dakar, fadar mulkin kasar Senegal. Babban taken taron shi ne “A karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kwararrun Sin da Afirka, domin inganta zamanintarwar Sin da Afirka”. Inda kwararru da masana, da jami’an gwamnati, da jakadu, da ‘yan jaridu da dai sauran wakilai daga bangarori daban daban na Sin da Afirka suka halarci taron.
Kafin bude taron, kwalejin nazarin Afirka ta kasar Sin da kwalejin nazarin hukumomin kasar Senegal sun kulla yarjejeniyar kafa cibiyar nazarin Sin da Afirka cikin hadin gwiwa.
- Rage Farashin Man Fetur Na Dangote Ya Sa Wasu Gidajen Mai Na Kullewa
- Zulum Ya Taya MNJTF Da Gwamnatin Alihini Bayan Harin Boko Haram A Wulgo
A yayin bikin bude taron, shugaban cibiyar nazarin ilmin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin, Gao Xiang ya ba da jawabi cewa, manufar taron ita ce, hada sassan nazarin ilmi na Sin da Afirka tare, domin inganta bunkasuwar kasashe masu tasowa cikin hadin gwiwa, tare da ba da gudummawa yadda ya kamata wajen gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani.
A nasa bangare kuma, firaministan kasar Senegal Ousmane Souko ya bayyana cewa, kasar Senegal tana son hadin gwiwa da cibiyar nazarin ilmin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin don kara cudanyar juna da gudanar da ayyukan nazarin ilmi tare, baya ga samar wa kasashen dake yammacin nahiyar Afirka dabarun neman samun ci gaba.
Bugu da kari, shugaban kwalejin nazarin hukumomin kasar Senegal ya ce, aikin kulla yarjejeniyar kafa cibiyar nazarin Sin da Afirka cikin hadin gwiwa, ya shaida yadda hadin gwiwar kwararru a tsakanin Sin da Afirka ya kai wani sabon matsayi. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp