A yau Laraba 7 ga watan nan ne aka bude taron kasa da kasa na baje kolin harkokin al’adu karo na 19 a birnin Shenzhen. Baje kolin dai zai gudana ne a tsawon yini 5.
A bana an tsara gudanar da shi ne ta zahiri, da kuma hadakar zahiri da yanar gizo, an kuma kara bunkasa adadin abubuwan da za a gudanar yayin baje kolin. Kaza lika an ware yankin baje kolin harkokin kasar Sin ta amfani da fasahohin zamani a karo na farko, da nufin yayata fannin masu ruwa da tsaki a masana’antar raya al’adu a matakin kasa, da kuma bangaren manyan dandaloli, da sabbin fasahohin kirkire-kirkire.
Kaza lika yayin gudanar sa, za a aiwatar da ayyuka da dama, kamar tarukan karawa juna sani, da dandaloli, da sanya hannu kan yarjeniyoyi, da ma takara mai ma’ana, don bunkasa ci gaban sashen raya al’adu na kasar Sin. (Saminu Alhassan)