Da safiyar yau Juma’a, aka bude taron koli karo na 7 na raya yanar gizo na kasar Sin, a birnin Fuzhou hedkwatar lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin, wanda aka mayar da “Habaka darajar bayanai da raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko” a matsayin babban takensa.
An shirya babban taron dandalin tattaunawa guda da ma kananan tarukan tattaunawa goma a yayin taron, inda aka gabatar da rahoton ci gaban kasar Sin a bangaren yanar gizo ta shekarar 2023, da ajiye daki mai fadin murabba’in mita dubu 56 wajen nuna sabon ci gaban da Sin ta samu a wannan fanni. (Amina Xu)