A yau ne aka bude babban taron layin dogo mai saurin gudu na duniya karo na 12, wanda zai dauki tsawon kwanaki hudu ana gudanarwa a babbar cibiyar taro ta kasa ta birnin Beijing na kasar Sin. Fiye da jami’an gwamnati, da jakadun kasashe a kasar Sin, da shugabannin kamfanoni, da kwararru da masana fiye da 2,000 daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 60, gami da wakilai na cikin gida ke halartar taron.
Taron ya mayar da hankali ne kan taken “Layin dogo mai saurin gudu: kirkire-kirkire da ci gaba suna inganta rayuwa”, da gina wani dandali na baje kolin nasarorin layin dogo mai saurin gudu, da musayar fasaha, da hadin gwiwar masana’antu a kasashe daban daban na duniya, tare da tattaunawa a kan manyan batutuwan sabbin hanyoyin samar da layukan dogo masu saurin falfala gudu a nan gaba.
Ƙungiyar sufurin layukan dogo ta duniya (UIC) ce ta kirkiro da taron na layin dogo mai saurin gudu, kuma ta dauki nauyin gudanar da shi a shekarar 1992. Ana gudanar da shi ne duk bayan shekaru biyu zuwa uku. An yi nasarar gudanar da shi har sau 11 zuwa yanzu, kuma yana da tasiri mai muhimmanci a fagen sha’anin jirgin kasa mai saurin gudu na duniya.
A bana ne ake cika shekaru 200 da samar da layin dogo a duniya. An kuma gudanar da taron layin dogo mai saurin gudu na duniya a birnin Beijing, wanda ya nuna cikakken matsayi mai muhimmanci, da bayar da fa’ida da kuma kyakkyawar gudummawar da aka samu daga layin dogo mai saurin gudu na kasar Sin wajen raya layin dogo mai saurin gudu a duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp