A yau Alhamis, aka bude taron ministoci na dandalin tattaunawa game da wayewar kai a duniya a birnin Beijing, inda aka mayar da hankali kan muhimmancin mabanbantan al’adu da fahimtar juna wajen samun ci gaban harkokin dan Adam.
Taron na yini biyu mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya” ya ja hankalin baki sama da 600 daga kasashe da yankuna 140.
Yayin wasu kananan taruka da za su gudana lokaci guda a karkashin dandalin, mahalarta za su lalubo muhimmiyar rawar da musayar al’adu daban-daban da fahimtar juna ka iya takawa ga ingiza dunkulalliyar duniya da inganta ci gaban duniyar da kwanciyar hankali da gadon al’adu da kirkire-kirkire da fahimta da abota tsakanin jama’a da samar da ci gaban kimiyya da fasaha da musaya tsakanin masana. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp