An bude taron mutum-mutumin inji na duniya na 2025 wanda zai dauki tsawon kwanaki 5, a yau 8 ga Agusta a birnin Beijing. Taron mai taken “kara wa mutum-mutumin inji hikima da kara wa jikin mutum-mutumin inji fasahohi”, ya ja hankalin fiye da kamfanoni 200 na mutum-mutumin inji na ciki da wajen kasar Sin, wadanda suka fito daga manyan masana’antu, inda adadin kamfanonin mutum-mutumin inji ya zama mafi girma a irin wannan taro a duniya.
An kasa wannan taro cikin manyan sassa uku da suka hada da “Ci gaban masana’antu”, “Amfani da kirkire kirkire”, da “Hadakar fasahohi”. Fiye da manyan masana kimiyya 400 daga ciki da wajen kasar Sin da wakilan kungiyoyin duniya da mambobin kwalejojin kimiyya, da ‘yan kasuwa za su tattauna batutuwan da suka shafi yanayin masana’antar mutum-mutumin inji da aikace-aikacen masana’antar da binciken fasaha.
- Sai Ƴan Siyasa Sun Haɗa Kansu Sannan Za Su Iya Tunkarar APC A 2027 – Lukman
- Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar
An baje kolin kayayyakin 1,500 daga kamfanoni fiye da 200, ciki har da sabbin samfura 100 da aka fara gabatarwa a duniya. Kamfanoni 50 na mutum-mutumin inji sun shiga wannan taron, wanda adadinsu ya zama mafi girma a irin wannan baje koli.
Sin ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na babbar kasuwar mutum-mutumin inji masu ayyukan masana’antu a duniya, wanda ta rike tsawon shekaru 12, kuma ita ce babbar kasa mai kera mutum-mutumin inji a duniya. Sin daya ce daga cikin kasashe masu samar da mutum-mutumin inji dake sahun gaba a duniya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a fannonin hidimar gida da masana’antu da kayan ajiya. (Amina Xu)