• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Bude Taron Shekara-shekara Na Majalisar Bada Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

An bude zama na biyu na taron majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC, da wajen karfe 3 na yammacin yau Litinin a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran jagororin kasar suka halarci zaman bude taron, kuma shugaban majalisar Wang Huning ya gabatar da rahoton aiki a madadin zaunannen kwamitin majalisar ta CPPCC. Rahoton da ta gabatar dai ya waiwayi ayyukan da majalisar ta gudanar a shekara daya da ta gabata, kana ya gabatar da shirin gudanar da ayyukan shekarar bana.

A yayin taron majalisar CPPCC na kwanaki 6, membobin majalisar fiye da dubu biyu, wadanda suka zo daga bangarori 34 za su saurari, tare da dudduba, da kuma tattauna kan rahoton aikin zaunannen kwamitin majalisar ta CPPCC, da rahoton daftarin ayyuka da aka gabatar, kana za su halarci taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, inda za su saurari, da tattauna rahoton aikin gwamnatin kasar, da bada shawara a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da zaman rayuwar jama’a da sauransu.

  • Me Ya Sa Amurka Ke Jin “Tsoron” Kasar Sin Har Da Na’urar Daga Kaya Da Ta Samar?
  • Xi Jinping Ya Taya Shehbaz Sharif Murnar Zama Firaministan Pakistan

Majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin wato CPPCC, tsari ne dake nuna salon musamman na kasar Sin, kana, muhimmiyar hukuma ce ta hadin-gwiwar jam’iyyu daban-daban gami da gudanar da shawarwarin siyasa a karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma, muhimmiyar hanya ce da ake bi wajen aiwatar da demokuradiyya daga dukkanin matakai a cikin harkokin siyasar kasar, kuma muhimmin bangare ne a cikin tsarin mulkin kasar.

Kwamiti na membobin kasa baki daya na CPPCC, kungiya ce dake aiwatar da tsarin CPPCC, wanda ke kunshe da wakilai daga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sauran jam’iyyun demokuradiyya da ba na kwaminis ba, da wadanda ba sa cikin kowace jam’iyya, da rukunonin al’umma, da wakilai daga kananan kabilu da bangarori daban-daban, da wakilan ‘yan uwanmu daga Taiwan da Hong Kong da Macau, da wakilan Sinawa mazauna kasashen waje da suka dawo da dai sauran wasu bakin da aka ba su goron gayyata na musamman. Manyan ayyukansu su ne, gudanar da shawarwari kan harkokin siyasa, da sa ido bisa tafarkin demokuradiyya, da kuma halartar harkokin siyasa da ba da shawarwari. Wadannan muhimman ayyukan uku sun nuna yadda ‘yan jam’iyyun siyasa gami da kungiyoyi daban-daban, da mutane daga kabilu da bangarori daban-daban suke shiga cikin harkokin kasa, gami da taka muhimmiyar rawarsu a cikin tsarin siyasar kasar Sin, kana, muhimmiyar alama ce dake bambanta majalisar CPPCC da sauran kungiyoyin siyasa.

Shekaru biyar ne wa’adin aikin kowane zagayen ‘yan majalisar CPPCC, kuma a kan gudanar da cikakken zamanta sau daya a kowace shekara. (Zainab Zhang/Murtala Zhang)

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

Ramadan: Sarkin Kano Ya Roƙi ‘Yan Kasuwa Da Su Taimaka Su Rage Farashin Kayan Abinci

LABARAI MASU NASABA

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Sin

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.