An bude zama na farko na taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 da safiyar yau Lahadi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, inda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnatin kasar.
Li ya yi nuni da cewa, Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki mai inganci da zaman lafiya a zamantakewar al’ummar kasar a shekarar 2022 yadda ya kamata, yana mai cewa, da wuya Sin ta samu sabbin nasarori a shekarar 2022.
Li ya ce, a shekarar bara, yawan GDPn kasar Sin ya karu da kashi 3 cikin dari, kuma karin wasu mutane miliyan 12 da dubu 60 sun samu aiki, kana farashin kayyayakin da jama’a suke kashe kudi kansu ya karu da kashi 2 cikin dari. Ya ce bisa sauyin yanayin mai sarkakiya da ake ciki, Sin ta cimma muhimmin burin samun bunkasuwar kasar na shekarar, yana mai cewa, Sin tana da karfin samun ci gaban tattalin arzikinta.
A cewar Li, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar, sun karu zuwa kudin Sin RMB yuan triliyan 121, kwatankwacin karuwar kaso 5.2 kan matsakaicin mataki cikin shekaru 5 da suka gabata, adadin da ya kai karuwar kusan yuan triliyan 70 cikin shekaru 10 da suka gabata, kimanin kaso 6.2 ke nan kan matsakaicin mataki. Firaministan ya kara da cewa, karfin tattalin arzikin kasar ya karu yadda ya kamata. Haka kuma, cikin shekaru 5 da suka gabata, manufar bude kofa ga ketare da yin gyare-gyare a gida ta kasar Sin ta ci gaba da zurfafa, haka kuma hadin gwiwa karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kara karfi, inda darajar kayayyakin da aka yi shige da ficensu ya zarce yuan triliyan 40, lamarin da ya sa kasar Sin ta kasance kan gaba a duniya wajen samun jarin kasashen waje da kuma zuba jari a ketare.
Firaminista Li ya ce, burin ci gaban tattalin arzikin kasar a bana shi ne, GDPnta ya karu da kimanin kashi 5 cikin dari. Ban da wannan kuma, Li ya gabatar da sauran burikan ci gaban kasar Sin na bana, wadanda suka hada da, yawan sabbin mutanen da za su samu aikin yi ya kai kimanin miliyan 12, adadin masu zaman kashe wando ya ragu zuwa kaso 5.5 bisa dari, sannan adadin karuwar farashin kayayyakin masarufi ya tsaya kan kaso 3 bisa dari. Kana saurin karuwar yawan kudin shiga da al’ummar Sin za ta samu ya yi daidai da saurin karuwar tattalin arzikin kasar, yayin da za a yi kokarin inganta cinikin shige da fice yadda ya kamata, da kokarin tabbatar da samun daidaito a harkokin cinikin waje. Bugu da kari, kasar Sin za ta yi kokarin cimma burin samar da yawan hatsin da ya wuce kilogiram biliyan 650, da rage amfani da kwal, man fetur, iskar gas, tare da ci gaba da kyautata muhallin halittu.
Rahoton aikin da Li ya gabatar ya kuma bayyana cewa, ya kamata a kara jawowa tare da amfani da jarin waje. Kasuwar kasar Sin mai bude kofa, za ta kara samar da dama ga bunkasuwar kamfanonin kasa da kasa dake kasar. Ya kamata a kara ba da iznin shiga kasuwar kasar, da kara bude kofa ga kasashen waje a fannin samar da hidima. Kana a kare hakkin kamfanoni masu jarin waje, da sa kaimi ga daddale yarjejeniyoyin tattalin arziki da cinikayya masu inganci kamar yarjejeniyar CPTPP ta kasashen yankin tekun Pasifik da ta shafi dukkan bangarori, da kuma fadada bude kofa ga kasashen waje bisa tsarin kasar.
Haka zakila ma dai, Li ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da martaba manufofin diflomassiya na tabbatar da ‘yancin kai da tafiyar da harkokinta da kanta da kuma tabbatar da zaman lafiya. Haka kuma, za ta bi hanyar neman samun bunkasuwa cikin lumana, da sada zumunta da hadin kai da kasa da kasa bisa ka’idoji biyar na zama tare cikin lumana, gami da martaba manufar bude kofa ga waje don moriyar juna da samun nasara tare. A ko da yaushe, kasar Sin na iyakar kokarinta wajen shimfida zaman lafiyar duniya, da bayar da gudummawa ga ci gaban duniya, da ma bin odar kasa da kasa.
Rahoton aikin ya kuma nuna cewa, kasar Sin na son hada gwiwa da kasa da kasa wajen aiwatar da shawarar ci gaban duniya, da ta tsaron duniya, da yada ra’ayin bai daya na darajar bil Adama, a kokarin kara azama ga raya makomar bil Adama ta bai daya, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.(Kande, Fa’iza, Zainab)