An bude yanki na farko na hedkwatar kungiyoyin kimiyya da fasaha na kasa da kasa a birnin Beijing, a jiya Laraba.
Zuwa yanzu, yankin wanda kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasar Sin da gwamnatin birnin Beijing suka gina, ya ja hankalin kungiyoyi 8, ciki har da kungiyar Society for Digital Earth, mai rajin amfani da sabbin fasahohin domin amfanin duniya da kuma kungiyar International Hydrogen Fuel Cell Association masu samar da makamashin Hydrogen.
A cewar Shu Wei, jami’in kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasar Sin, manufar yankin ita ce hada nasarorin da Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha da nasarorin da sauran sassan duniya suka samu a fannin, cikin aminci.
Shu Wei ya kuma bayyana yakinin wannan yanki zai saukakawa masana kimiyya da fasaha na kasar Sin shiga ana damawa da su a harkokin duniya. Haka kuma zai bayar da gudunmuwa wajen tsare gaskiya da tabbatar da aminci da hadin gwiwa a tsakanin masana kimiyya da fasaha na kasashen duniya. (Fa’iza)