• Leadership Hausa
Sunday, October 1, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Tatsuniyoyi Guda Hudu Na Sin

by CMG Hausa
4 months ago
in Daga Kasar Sin
0
Manyan Tatsuniyoyi Guda Hudu Na Sin

Wasan kwaikwayo na Kun mai suna Liangzhu

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Manyan tatsuniyoyi guda hudu na Sin na nufin tatsuniyoyi hudu da aka yada baka da baka ko a rubuce kan takarda da dai sauransu a kasar Sin, wadanda suka fi yin tasiri. Wadannan tatsuniyoyi hudu da dai sauransu sun zama wani muhimmin kashi na adabin jama’ar kasar Sin. Dukkan tatsuniyoyin hudu sun bayyana labaran soyayya. Wannan ya bayyana amincewar jama’a ga hakikanin soyayya.

Wata mace kirar Mengjiangnv
A yayin daular Qin, akwai wata mace mai kyan gani sosai, a kan kira ta Mengjiangnv. Ta shiga cikin soyayya tare da Fan Xiliang bayan da suka gamu da juna a karo na farko. Sai bayan samun amincewar iyayensu, su biyu sun shirya aure. Amma a daidai wannan lokaci, sarki Qinshihuang yana share fagen gina babbar ganuwa, shi ya sa sojojinsa sun kama mutane a ko ina domin gina ganuwar. A ranar aurensu kuma, sun cafke Fan Xiliang bisa karfi, har sun tura shi zuwa wani wuri mai nisa sosai domin gudanar da aiki. Mengjiangnv ta yi bakin ciki kwarai da gaske tare da yin fushi, tana begen mijinta sosai. A kai a kai, lokacin sanyi ya yi. Mengjiangnv ta samar da tufafin kaucewa sanyi, ta je ta nemi mijinta a babbar ganuwa.

Tatsuniyoyi
Hasumiyar Leifeng dake gabar tabkin Xihu a birnin Hangzhou

Bayan sha wahalhalu masu dimbin yawa, Mengjiangnv ta isa babbar ganuwa a karshe. Amma a wannan wuri, ta ga ganuwa kawai a maimakon mijinta. Daga bisani, ta samu labari da cewa, Fan Xiliang ya riga ya mutu a sakamakon yawan aiki, an binne shi a kofar babbar ganuwa. Da ganin haka, Mengjiangnv ta yi kuka. Hawayenta sun yi kama da ruwan sama ba tare da kasala ba har na tsawon kwanaki uku. Hakan ya burge sararin sama da kasa, har ma ta lalata babbar ganuwa kilomita 400. Gawar mijinta ta fito daga buraguzan babbar ganuwa. A karshe ta samu damar ganinsa a karo na karshe.

Wata mace mai suna Bai Suzhen da mijinta mai suna Xu Xian
A yayin ranar Qingming ta kasar Sin, birnin Hangzhou cike yake da furanni masu launin ja da itatuwan Willow masu launin kore da tabki da duwatsu, wadanda suke da kyan gani sosai. Dodannin macizai mata biyu masu suna Bai Suzhen da Xiaoqing sun kai ziyara a wannan wuri. An yi ruwan sama. Su biyu sun gamu da wani matashi mai suna Xu Xian ta hanyar aron laima. Bai Suzhen da Xu Xian sun fada cikin soyayya. Ba da dadewa ba, sun yi aure, sun bude wani kantin sayar da magunguna tare da ba da jiyya. Suna jin dadin zaman rayuwa sosai.

Tatsuniyoyi
Wasan kwaikwayo na Huangmeixi mai suna Niulang da Zhinv

Amma wani sufi mai suna Fahai dake gidan ibada na Jinshan ya tarar da lamarin, sai ya yi kokarin raba su. Da farko, ya gaya wa Xu Xian matsayin matarsa na wata dodanniyar macijiya, tare da tsara wani shiri, ta haka Bai Suzhen ta bayyana hakikanin jikinta na macijiya. Daga bisani, Fahai ya cafke Xu Xian a gidan ibadan Jinshan. Bai Suzhen da Xiaoqing sun isa gidan ibada, sun roki Fahai da ya saki Xu Xian, amma ba tare da samun nasara ba. A sabili da haka, Bai Suzhen ta haifar da ambaliyar ruwa, ta yi gwagwarmaya da Fahai. Amma sabo da ta sami ciki, shi ya sa ta sha kaye a karshe. Fahai ya karbe ta a kwanonsa na zinariya, ya dasa shi a karkashin tatsuniyar Leifeng dake dab da tabkin Xihu. A sakamakon haka, an raba masoya biyu.

Labarai Masu Nasaba

“Mafarkina Na Zuwa Sararin Samaniya” 

Yadda Sin Ta Kubuta Daga “Kangin Talauci”

Tatsuniyoyi
Wasan kwaikwayo na Sichuan-Labarin macijiya Bai Suzhen

Daga baya, Xiaoqing ta tsere daga gidan ibada na Qingshan, ta samu horo yadda ya kamata. A karshe, ta ci nasarar Fahai, ta tilasta masa zuwa jikin kaguwa. Sai ta ceci Bai Suzhen daga karkashin tatsuniyar Leifeng. Daga bisani, Bai Suzhen da Xu Xian sun sake yin zama tare.
A cikin wannan labari, an samar da wata dodanniyar macijiya mai kyan gani da jin tausayi, tare da nuna babban yabo ga soyayya mai kyau.

Matashi Niulang da matarsa Zhinv
An ce a zamanin da da can, akwai wani matashi mai jin tausayi dake kiwon shanu, yana fama da talauci. Wata rana, bisa taimakon wani tsohon sa, ya gamu da wata waliyin sararin sama mai suna Zhinv. Zhinv ya fada cikin soyayya da wannan matashi mai kiwon shanu, sai sun yi aure. Daga bisani, Zhinv ta haifi ‘ya’ya biyu, wato wani jariri da wata jaririya. Suna jin dadin zaman duniya.

Tatsuniyoyi
Wasan Opera na Beijing-Labari macijiya Bai Suzhen

Amma ba zato ba tsammani, mahaifin Zhinv ya yi fushi a sakamakon lamarin. Matar sarkin sararin sama mai suna Wangmu(Wangmu: wata waliyin sama ce ta zamanin da, wadda take da babban iko) ta ba da umurni ga Zhinv da ta koma fadar sama nan take. Ko da yake ba ta so ta koma ba, amma babu yadda za ta yi, sai Zhinv ta tafi ba tare da miji da ‘ya’yanta ba, ta tashi bisa gajimare. Matashi mai kiwon shanu ya yi bakin ciki, ya bi matarsa tare da ‘ya’ya biyu bisa taimakon tsohon sa. Wangmu ba ta iya hana su ba, sai ta yi amfani da fasaharta, ta samar da wani kogin taurari mai fadi a tsakaninsu.

Tatsuniyoyi
Wasan Yue mai suna Liangzhu wanda ya bayyana labarin Liang Shanbo da Zhu Yingtai

Daga baya, Niulang da Zhinv su kan hangen juna a gabobi biyu na kogin taurari. Amma wannan ba zai rage soyayyar dake tsakaninsu ko kadan ba. A ran 7 ga watan Yuli na kowace shekara bisa kalandar noma, dubu-dubun tsuntsayen Magpie sun zo sun kafa wata gada bisa jikuna a kan kogin taurari. Sai wannan iyali na iya haduwa. A sakamakon haka, wannan rana ta kasance ranar bayyana soyayya da ba da kyauta ga masoya, ma iya cewa, wannan ne ranar soyayya ta yankin gabas. An ce a wannan rana, idan ka zauna a karkashin bishiyoyin inabi, ka yi shiru ka saurara, kana iya saurari abubuwan da suke magana a kan gadar tsuntsayen Magpie.

Liang Shanbo da Zhu Yingtai
An ce a da can, akwai wata mace mai hikima da kyan gani, sunanta Zhu Yingtai. Amma a wancan lokaci, an nuna rashin amincewa ga mata da su shiga makaranta. A kokarin samun damar koyon ilmi, Zhu Yingtai da wata yarinya mai ba da hidima sun yi adon maza, sun shiga makarantar dake birnin Hangzhou.
A wannan wuri, Zhu Yingtai ta gamu da Liang Shanbo, wanda yake da ilmi mai zurfi kana mai kirki sosai. Su biyu sun yi alkawarin zama ‘yan uwa. Akwai dankon zumunci a tsakaninsu.

Tatsuniyoyi
Wasan Yue mai suna Liangzhu

Shekaru sun wuce, wa’adin karatun Zhu Yingta ya cika. Sai ta yi ban kwana da malamai ta koma gida. Amma a daidai wannan lokaci, Zhu Yingtai ta kaunaci Liang Shanbo sosai. Liang Shanbo kuma ba shi da wata masaniya. Ya nuna girmamawa ga Zhu Yingtai. Sai sun yi ban kwana da juna. Zhu Yingtai ta yi karya da cewa, tana da wata karamar ‘yar uwa. Tana so Liang Shanbo ya yi aure da ita. Daga bisani, Liang Shanbo ya kai ziyara a gidan Zhu Yingtai. Amma mahaifinta ya riga ya tilasta diyarsa da ta auri wani dan mai kudi Ma Wencai. Liang Shanbo da Zhu Yingtai sun gamu da juna sun yi bakin ciki domin rashin damar aure. Bayan da ya koma gida, Liang Shanbo ya yi bakin ciki sosai, har ya kamu da cuta. Ba da dadewa ba ya mutu a sakamakon haka.

Tatsuniyoyi
Zanen Mengjiangnv

Zhu Yingtai ba ta da karfin canza wannan lamari ba, sai ta auri Ma Wencai. A daidai ranar auren, Zhu Yingtai ta bukaci kai ziyara a kabarin Liang Shanbo domin yin addu’a. Ba zato ba tsammani, an kada iska tare da muryar tsawa. Kabarin Liang Shanbo ya bude, Zhu Yingtai ta fada a ciki tare da yin murmushi. Sai an yi rana nan take, furanni da yawa sun sheki. Liang Shanbo da Zhu Yingtai sun zama malam-bude-littafi guda biyu, sun yi zama tare.

Wannan labari sun bayyana jarumtakar matasa ta neman soyayya a zamanin da, tare da nuna rashin amincewa ga aure irin na tilastawa da burin samun rayuwa mai jin dadi.(Amina Xu daga sashen Hausa na CMG)

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Bude Yanki Na Farko Na Hedkwatar Kungiyoyin Kimiyya Da Fasaha Na Kasa Da Kasa A Beijing

Next Post

Shugaban Nijeriya Na 16: Jan Aikin Da Ke Gaban Jagaban

Related

“Mafarkina Na Zuwa Sararin Samaniya” 
Daga Kasar Sin

“Mafarkina Na Zuwa Sararin Samaniya” 

6 days ago
Yadda Sin Ta Kubuta Daga “Kangin Talauci”
Daga Kasar Sin

Yadda Sin Ta Kubuta Daga “Kangin Talauci”

1 month ago
Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa 
Daga Kasar Sin

Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa 

1 month ago
Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa 
Daga Kasar Sin

Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa 

1 month ago
Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa: Yadda Ake Yada Akidun Confucius Na Tsawon Sama Da Shekaru 2,000
Daga Kasar Sin

Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa: Yadda Ake Yada Akidun Confucius Na Tsawon Sama Da Shekaru 2,000

2 months ago
Yadda Ake Fahimtar Ma’anar Alfahari Da Al’adun Kasar Sin Daga Dakin Ibadar Three-Su
Daga Kasar Sin

Yadda Ake Fahimtar Ma’anar Alfahari Da Al’adun Kasar Sin Daga Dakin Ibadar Three-Su

2 months ago
Next Post
Cire Tallafin Man Fetur Ba Nan Take Zai Fara Aiki Ba, Sai Karshen Watan Yuni – Tinubu 

Shugaban Nijeriya Na 16: Jan Aikin Da Ke Gaban Jagaban

LABARAI MASU NASABA

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

October 1, 2023
Tatsuniyoyi

Ranar ‘Yanci: Tinubu Ya Kara Wa Kananan Ma’aikata N25,000 Kan Albashinsu

October 1, 2023
Hangzhou

Birnin Hangzhou Ya Samu Karuwar Masu Yawon Bude Ido Albarkacin Gasar Wasanni Ta Asiya Dake Gudana

October 1, 2023
Syria

Shugaban Syria: Manyan Tsare-tsare Uku Na duniya Su Ne Jagororin Sabuwar Duniya

October 1, 2023
BUA

Daga Gobe 2 Ga Oktoba Farashin Buhun Simintin BUA Ya Koma N3,500 – Kamfanin

October 1, 2023
Kasar Sin

Ofishin Jakadancin Kasar Sin Dake Najeriya Ya Shirya Bikin Murnar Cikar Sin Shekaru 74 Da Kafuwa

October 1, 2023
Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

October 1, 2023
Amurka

Amurka Ita Ce “Daular Karya”Ta Ko Wace Fuska

October 1, 2023
Gwamnatin Tarayya Ta Yaba Da Ayyukan Bello Koko Na Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kafa Sashi Na Musamman A NPA Don Inganta Ayyukanta

October 1, 2023
Dambe: An Fafata Tsakanin Dan Aliyu Da Rabe Shagon Ebola

Dambe: An Fafata Tsakanin Dan Aliyu Da Rabe Shagon Ebola

October 1, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.