A kwanakin baya, aka buga wasu littattafai hudu dake bayyana yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ke aiki a kananan hukumomi, ciki har da mai taken “A taimakawa jama’a kyautata zaman rayuwarsu–yadda Xi Jinping ya yi aiki a Zhengding” da dai sauransu.
Littattafan guda hudu, sun mayar da hankali ne kan yadda Xi Jinping ya jagoranta tare da inganta gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da kuma zamanintar da kananan hukumomin da ya taba yi wa aiki.
Kana an waiwayi yadda Xi Jinping yake gudanar da harkokin mulki tare da yadda yake mayar da hankali kan dukkan bangarori, da yadda yake da hangen nesa, da kulawa da zaman rayuwar jama’a, da tsare gaskiya da aiki tukuru, da jajircewa wajen yin kirkire-kirkire, da kuma sauke nauyin dake wuyansa.
Kazalika an yi cikakken bayani game da akidar Xi Jinping, da yadda yake mayar da hankali kan jama’a, da yanayin tunaninsa, da halinsa da kuma nasarar da ya cimma ta ban mamaki a ayyukansa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)