Bayan musayar wuta da masu garkuwa da mutane, hadin guiwar jami’an ‘yansanda da ‘yan sintiri, sun ceto mutum uku a yankin Aboto da ke a karamar hukumar Asa a jihar Kwara.
Shugaban kungiyar ‘yan sintiri na jihar Kwara Saka Ibrahim ne, ya tabbatar da kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su.
Ya bayyana cewa, daga cikin mutum ukun da aka kubutar, akwai wani dan sintiri daya mai suna Muiz Isiaka, inda ya ce, an sace su ne a wurare daban-daban a makon da ya gabata.
Ibrahim ya kara da cewa, an yi garkuwa da Muiz ne, a kan hanya a lokacin da ya dauko surukansa zuwa gida bayan sun halarci taron radin sunan jaririn da aka haifa masa.
Shugaban ya ce, an ceto mutum ukun ne, da misalin karfe 2 na dare, bayan ‘yansanda sun yi musayar wuta da su, an kubutar da su duka ba tare da biyan kudin fansa ko sisi ba.