Gwamnatin jihar Kogi ta ce ta yi nasarar kuɓutar da sauran ɗalibai takwas na jami’ar Confluence University of Science and Technology (CUSTECH) Osara da aka yi garkuwa da su a farkon watan da ya gabata, wanda ya kawo adadin daliban da aka ceto zuwa 30.
Wani abin takaici, masu garkuwa da mutanen sun kashe ɗalibai biyu a lokacin da gwamnati ta ki biyan kuɗin fansa.
- Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Zai Gabatar Da Kansa A Gaban Kotu Ranar 13 Ga Watan Yuni
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2 Daga Daliban Da Suka Sace A Kogi
Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kingsley Fanwo ne ya sanar da hakan. Ya bayyana cewa Gwamna Ahmed Usman Ododo ya ba da umarnin bayar da cikakken goyon baya don dawo da ɗaliban da aka ceto ga iyalansu, tare da aiwatar da matakan inganta tsaro a jihar Kogi.
Gwamnan ya miƙa godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, da manyan jami’an Soji da na tsaro bisa rawar da suka taka wajen aikin ceto ɗaliban.
Ya kuma mika godiyarsa ga gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazak bisa haɗin kai da goyon baya.