Rundunar ‘yansandan Jihar Kuros Riba ta tabbatar da kubutar da wasu ‘yansanda uku da wasu matasan unguwa suka yi tsare su.
Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Irene Ugbo, ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai (NAN), a garin Kalaba a ranar Talata.
- NEMA Ta Karbi ‘Yan Nijeriya 137 Da Suka Makale A Kasar Libya
- Sin Na Da Aniyar Cimma Nasarar Yaki Da Cin Hanci Da Karbar Rashawa
Ta ce wasu matasa ne suka yi garkuwa da jami’an a Ndon Owong da ke karamar hukumar Odukpani a jihar a yayin da suke gudanar da aiki.
Ugbo ta ce a ranar Litinin din da ta gabata ne jami’an da ke yaki da masu garkuwa da mutane karkashin jagorancin,SP Awodi Abdulhameed suka kubutar da jami’an.
Idan dai za a iya tunawa an kashe mutane biyar tare da birne su a wani rami bisa zargin maita.
Ana zargin wasu matasa a unguwar ne suka kashe su da suka zarge su da aikata munanan ayyuka a Ndon Owong.
A halin da ake ciki, Ugbo ta ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a sace jami’an da kuma kisan mutane biyar din.
“Ba wanda zai iya daukar doka a hannunsa, kundin tsarin mulkinmu bai amince da wani abu maita ba. Idan suna da wani abu, ya kamata su bi hanyar da ta dace don magance lamarin ba wai kashe rayukan mutane marasa laifi ba.
“An kashe mutane biyar din ta mummunan hanyar kisan gilla kuma aka birne su a wani rami a cikin daji.
“Wannan dabbanci ne, ba za a yarda da shi ba kuma ba za mu bar wani abu ba don tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun fuskanci cdoka,” in ji ta.