A yau Lahadi 28 ga wata ne Turkawa suka fara kada kuri’a a zagaye na 2 na zaben shugaban kasar.
Erdogan ya kara da abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu a zagayen farko na ranar 14 ga watan Mayu. Amma ya gaza samun kashi 50% da ake bukata domin kaucewa shiga zagaye na biyu na zaben.
An fara kada kuri’a ne da karfe 8 na safe (0500 GMT) kuma za a kammala da karfe 5 na yamma. (1400 GMT).