An ci kamfanin manhajar TikTok tarar fam miliyan 12.7 sabida amfani da bayanan yara ‘yan kasa da shekara 13 ba tare da izinin iyayensu ba, a cewar wani bincike da Ofishin Kwamishinan Yada Labaran kasar (ICO) ya fitar.
Kwamishinan yada labarai na Burtaniya, John Edwards, ya shaida wa BBC cewa: “Akwai dokoki da aka kafa don tabbatar da cewa yaranmu suna cikin tsaro a duniyar komfuta (digital) kamar yadda suke cikin tsaro a duniyarmu. TikTok ya saba wadannan dokokin.
“Kamfanin TikTok yaba wa yara ‘yan kasa da shekaru 13 kimanin miliyan daya damar amfani da manhajar ba ta hanyar da ta dace ba kuma TikTok yana tattara bayanansu ya yi aiki da su.
“Wannan izina ce. TikTok yakamata ya sake shirya kansa. Tarar da muka yi masa ta fam miliyan £12.7 ya nuna cewa, dagaske muke wurin kiyaye yaranmu.”
Wannan tara da ofishin kwamishinan yada labarai na kasar Burtaniya ya yi wa TikTok, na daya daga cikin manyan tara da ofishin ya yi.