• English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Daddale Tarin Yarjejeniyoyi Yayin Taron Baje Kolin Harkokin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afirka

byCGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
inDaga Birnin Sin
0
An Daddale Tarin Yarjejeniyoyi Yayin Taron Baje Kolin Harkokin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afirka

An daddale yarjejeniyoyi masu tarin yawa a yayin taron baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu da aka kammala jiya Lahadi 15 ga watan nan, a gabar da sassan biyu ke kara zurfafa hadin gwiwarsu.

Kwamitin tsara baje kolin ya sanar da cewa, an sanya hannu kan yarjejeniyoyi na gudanar da ayyuka 176 da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 11.39. Alkaluman karuwar adadin ayyukan da aka amince za a aiwatar sun karu da kaso 45.8 bisa dari, yayin da na kudaden gudanar da ayyukan suka karu da kaso 10.6 bisa dari kan na shekarar 2023.

Ya zuwa tsakar ranar jiyan, sama da mutane 200,000 sun ziyarci harabar baje kolin da aka kammala a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, adadin da ya rubanya wanda aka gani a taron da ya gabaci na bana.

Har ila yau a karon farko, baje kolin ya kunshi nune-nunen hajojin hadin gwiwar kamfanonin Sin da na kasashen Afirka, da kayayyaki masu inganci na Afirka, da kayayyakin kawa na masana’antun Sin da Afirka.

Kusan kamfanoni 2,100, da suka hada da 764 daga kasashen Afika 43 ne suka halarci baje kolin. Yayin da masu sayayya daga Sin da sauran sassan kasa da kasa 12,000 suka halarci bikin.

Labarai Masu Nasaba

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka

Kazalika, cikin kwanaki hudu da aka kwashe ana gudanar da baje kolin, an sayar da nau’o’in albarkatun gona na nahiyar Afirka sama da 200 ta intanet da kuma manyan shaguna. Bugu da kari, wasu kasashen Afirka 14 sun gudanar da wasu ayyukan musamman na yayata hada-hadar tattalin arziki da cinikayya a yayin baje kolin. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare
CGTN Hausa and Sulaiman

CGTN Hausa and Sulaiman

Related

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   
Daga Birnin Sin

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

18 hours ago
Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka
Daga Birnin Sin

Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka

19 hours ago
Nazari Ya Gano Falalen Dutse Na Yanki Mai Nisa A Duniyar Wata Ya Fi Tsananin Sanyi Fiye Da Na Yanki Na Kusa
Daga Birnin Sin

Nazari Ya Gano Falalen Dutse Na Yanki Mai Nisa A Duniyar Wata Ya Fi Tsananin Sanyi Fiye Da Na Yanki Na Kusa

20 hours ago
Next Post
Sin Ta Yi Kira Ga Iran Da Isra’ila Su Dauki Matakan Dakile Ruruwar Wutar Rikicinsu Nan Da Nan

Sin Ta Yi Kira Ga Iran Da Isra’ila Su Dauki Matakan Dakile Ruruwar Wutar Rikicinsu Nan Da Nan

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

October 7, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

October 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025
Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

October 6, 2025
Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

October 6, 2025
Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka

Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka

October 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.