Hukumar kwallon kafar Italiya, ta dakatar da Dan wasa Nicolo Fagioli tsawon watanni bakwai, bayan an same shi da karya dokar caca.
An samu Fagioli da yin caca a wasannin da kuma yin wasu abubuwan da aka haramta wa duk kwararren dan kwallo yi.
- Messi Ya Jefa Kwallaye Biyu Yayin Da Argentina Ta Samu Nasara Akan Peru
- Ronaldo Ya Jefa Kwallo Biyu Yayin Da Portugal Ta Lallasa Bosnia Da Ci 5-0
Kamar yadda hukumar ta bayyana, laifin nasa na dakatarwa ne har tsawon shekara daya, amma daga baya ta yi masa sassauci.
Fagioli, mai shekara 22, zai yi aikin kyauta tsawon watanni biyar a hukumar da ke kula da ‘yan kwallo masu tasowa.
Da wannan hukuncin, dan wasan ba zai yiwa Juventus wasa ba, wadda tun farko aka dakatar mata da Paul Pogba a kan laifin shan abubuwan kara kuzari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp