Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya dakatar da Sarkin Birnin ‘Yandoto, Aliyu Marafa, bisa bada sarautar Sarkin Fulani ga kasurgumin shugaban ‘yan fashin daji da ake nema ruwa a jallo, Adamu Aliero-Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero.
Matakin da Masarautar ta dauka ya jawo bacin rai, inda jama’a da dama suka yi Allah wadai da irin karramawar da aka yi wa masu aikata laifuka.
- Hajjin 2022: Alhazan Bangladesh 88 Ne Suka Rasu A Saudiyya
- NDLEA Ta Damke Wata Mata Za Ta Yi Safarar Miyagun Kwayoyi Zuwa Oman
Sai dai a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya fitar, gwamnatin ta barranta kanta daga matakin na Sarkin, inda ta dakatar da shi, tare da kafa kwamitin da zai binciki lamarin.
Kuma gwamnatin ta bada rikon sarautar ga Alhaji Mahe Garba Marafa, Hakimin ‘Yandoto.
Sai dai kuma masarautar ‘Yandoton ta ce ta dauki matakin nadin sarautar ne domin kawo zaman lafiya a ya kin na Tsafe da makwabtan yankin.
A jiya Lahadi an ruwaito cewa cincirindon al’umma ne su ka halarci bikin nadin sarautar da Sarkin ya yi wa Ado Aliero, duk kuwa da cewa a shekaru biyu da su ka gabatar rundunar ‘yan sanda ta sanya ladan Naira miliyan 5 ga duk wanda ya gano inda ya ke.
Rahotanni sun bayyana cewa shi dai Ado Aliero, shi ne babban dan fashin dajin da ya addabi jihohin Zamfara da Katsina.